--
Sakon Bidiyo: A karo na biyu; El-Rufa'i ya sake killace kansa saboda annobar korona

Sakon Bidiyo: A karo na biyu; El-Rufa'i ya sake killace kansa saboda annobar korona

Alkaluma da ke fitowa kwanakin baya bayan nan na nuna hauhawar adadin 'yan Nigeria da ke kamuwa da cutar korona 


A cikin makon nan ne gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya sanar da cewa zai sake saka dokar kulle idan jama'a ba su kiyaye, sun bi doka ba 



El-Rufa'i, a cikin wani sakon bidiyo da ya wallafa a daren ranar Juma'a, ya sanar da cewa ya killace kansa Gwamnan jihar Kaduna, 


Mallam Nasir El-Rufa'i, ya sanar da cewa ya sake killace kansa bayan wasu na hannun damarsa da hadimansa sun kamu da kwayar cutar korona, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na tuwita. 


El-Rufa'i ya sanar da hakan ne a wani sakon faifan bidiyo da ya wallafa a daren ranar Juma'a. 


A cewarsa, ya killace kansa ne biyo bayan samun rahoton cewa wasu na hannun damarsa da makusanta iyalinsa sun kamu da kwayar cutar korona, kuma sun yi cudanya kafin fitowar sakamakon gwajinsu.


 


A ranar Alhamis ne El-Rufa'i ya ce akwai yiwuwar zai sake saka dokar kulle saboda hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da ake samu a jihar da fadin kasa. 


Abdallah Yunus Abdallah, mai taimakawa El-Rufa'i a bangaren watsa labarai, ya ce gwamnati za ta dauki wannan mataki ne saboda kare hakkin kare rayukan mutanen jihar ya rataya ne a wuyan gwamnan. 


A cewarsa, gwamnan ya yi wannan jan kunnen ne saboda alhakinsa ne ya kula da lafiyar mutanen jihar Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta rawaito. 


Hadimin gwamnan ya kara da cewa babu abinda zai hana gwamnan Kaduna ya sake saka dokar kullen jama'a matukar basu kiyaye sharudan kare kai domin dakile yaduwar cutar ba ko kuma idan alkaluman masu kamuwa da cutar suka cigaba da hauhawa. 


"Yaki da cutar korona aiki ne da ya rataya a wuyan dukan jama'a, ba iya gwamnati kadai ba, a saboda haka ya zama wajibi a kan mutane su kula tare da yin biyayya ga dokoki da matakan kare kai domin dakile yaduwar cutar," a cewarsa. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Sakon Bidiyo: A karo na biyu; El-Rufa'i ya sake killace kansa saboda annobar korona"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?