Rufe Layukan Waya: Kamfanin Sadarwa na MTN Da Airtel Sun bayar da link din da mutane zasu shiga dan su hada layin su da National I.D card
Kamfanin Sadarwa na MTN ya bayar da link din da mutane zasu shiga dan su hada layin su da National I.D card, ta yadda ba sai sun je Ofis din su ba.
Abubuwan Da Ake Buqata Domin hađa lambar waya da NIN sun hađa da :
1. Full name, wanda yake kan National I.D Card.
2. Phone number.
3. Email.
4. NIN (National Identification Number).
Bayan ka tanadesu sai ki shiga wannan adireshin 👉 https://www.mtnonline.com/nim/ ko kuma danna nan domin zuwa ga shafin,
Bayan ka shiga adireshin zai kawoka wannan shafin da ke kasa 👇
Sai ka shigar da abubuwan da aka buqata, Bayan ka shigar da abubuwan da aka buqata, sai ka danna SUBMIT, Zai kawoka zuwa ga wannan shafin da ke kasa 👇
Zaka sami saqo ta lambar wayar da ka shigar na wasu lambobi guda 5 wato ONE TIME PASSWORD (OTP),
Sai ka shigar da su a wajen da aka rubuta enter OTP, sai ka danna SUBMIT.
Bayan da danna SUBMIT zai kawoka zuwa ga wannan shafin da ke kasa wanda shikenan ka gama hađa phone number đinka da NIN
SOURCE: BZGLOBALSERVICE.COM.NG
0 Response to "Rufe Layukan Waya: Kamfanin Sadarwa na MTN Da Airtel Sun bayar da link din da mutane zasu shiga dan su hada layin su da National I.D card"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?