Rufe layikan waya: 'Yan Najeriya sun koka a kan N20 na duba NIN
A ranar Litinin minista Pantami ya bayar da umarnin duba NIN ta hanyar *346#, ko kuma a rufe layin wayar mutum
Tun bayan nan 'yan Najeriya suka shiga caccakar ma'aikatar sadarwa a kan N20 din da za a cire musu idan za su duba NIN
Wasu gani suke yi wata sabuwar hanyar damfara ce ma'aikatar ta bullo da ita, don haka suka yi ta korafi wasu suka ki yi Bayan gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwa a kan rufe duk wani layin waya wadanda ba a hada shi da lambar katin dan kasar mai shi ba, wato NIN, daga ranar 30 ga watan Disamba.
Mutane da dama sun rikice a kan N20 din da za su yi amfani da ita don duba NIN din ta hanyar kiran *346#, Vanguard ta wallafa. Umarnin rufe katin wayar yazo ne bayan taron gaggawa da masu ruwa da tsaki suka yi na kamfanin sadarwa da ministan sadarwa, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, a ranar Litinin, 14 ga watan Disamban 2020.
Bayan doguwar tattaunawar ne aka samar da shawarar wajabta hada layuka da NIN. Daga nan ne 'yan Najeriya suka yi ta cece-kuce a Twitter. Wani MrOdanz cewa yayi, "Lallai wannan salon damfara ne. A kalla mutane miliyan 100 za su yi, idan ka kirga N20 sau miliyan 100, ya kuke gani?"
AishaYesufu ta ce "Da N20 din da na dage na wahala na samu, ina ganin za su cire N20 na hakura da yi. Na ari wani katin a hannun wasu idan zan yi amfani dashi." Wata JoyMicah ta ce "Na shiga layin wadanda aka damfara N20. Gaskiya an cuceni kuma an damfareni."
fkabudu yace "Oho. Nidai nasan dole sai an ciri kudi. Ka kirga N20 sau yawan 'yan Najeriya." Wata derra_o ta ce, "Na so duba na layina, amma sai naga sai an cire N20. Shine na fasa yi. Kun dade baku rufe katin nawa ba."
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Rufe layikan waya: 'Yan Najeriya sun koka a kan N20 na duba NIN "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?