PSC ta kori manyan 'yan sanda hudu daga aiki; CSP, DSP 2, da ASP duba dalili
Hukumar kula da aikin 'dan sanda (PSC) ta amince da sallamar wasu manyan jami'an rundunar 'yan sanda daga aiki - PSC ta sanar da cewa ta sallami jami'an daga aiki ne bayan samunsu da aikata laifuka daban-daban da suka sabawa aikin dan sanda
Daga cikinsu akwai jami'an ada aka samu da laifin safarar muggan makamai zuwa cikin Nigeria Hukumar kula da ayyukan yan sanda (PSC) ta sanar da sallami wasu manyan jami'an rundunar 'yan sanda guda huɗu bisa laifukan da suka shafi cin amana da nuna rashin kwarewa a aiki.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da shugaban hukumar, Ikechukwu Ani, ya fitar tare da aika sako zuwa ga manema labarai a yau, Lahadi, a Jihar Lagos, kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.
KUKARANTA:Dawowar korona: El-Rufa'i y umarci rukunin wasu ma'aikata su fara aiki daga gida daga Ranar Litinin
Mr Ani ya ce, hukumar ta ɗauki wannan mataki yayin wani zaman ganawa da hukumar ta yi ranar Juma'ar da ta gabata. “An sallami babban Sufuritanda (CSP) na 'yan sanda bisa rashin gaskiya da nuna halayen da suka da na jami'in tsaro.
"Sannan an kara sallami wani jami'in dan sanda mai mukamin Sufuritanda (SP) bayan samunsa da laifin haɗa baki tare da wasu batagari guda hudu domin sace na'urar rarraba hasken wutar lantarki a unguwa; wato taransifoma.
"Kazalika, PCS ta bayar da umarnin a gurfanar da shi saboda rasin gaskiyar da ya nuna da kuma cin amanar aikin dan sanda. “Sai kuma karin wasu manyan jami'an guda biyu da suka hada da babban mataimakan sufuritanda (DSP) da mataimakin Sufuritanda (ASP), a cewar Ani.
Ani ya kara da cewa; “mataimakin Sufuritandan (ASP) ya jagoranci shigo da makamai ta barauniyar hanya daga kasar Benin. "Shi kuwa DSP an same shi da laifin fitar da wasikar bogi domin rakiyar wata kwambar motocin SARS da zummar an sake su ne a hukumance.
"Sa'ar da aka yi lokacin sojoji na kan aikin bincike kan hanyar da suka je wucewa, suka binciki kayan dake cikin motocin. DSP din da abokan laifinsa sun tsere, sun bar motocin a nan." Ani ya tabbatar da cewa kowanne cikin su zai fuskanci fushin hukuma.
Source: Legit
0 Response to "PSC ta kori manyan 'yan sanda hudu daga aiki; CSP, DSP 2, da ASP duba dalili"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?