Na halaka mahaifiyata ne saboda mayya ce, Sojan da ya tsere daga wurin aiki
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta damke wani soja mai mukamin Kofur da laifin kisan mahaifiyarsa
Charles Thompson ya saba dukan mahaifiyarsa a duk lokacin da fada ya hada su amma sai ya soka mata wuka a ranar
Sojan da ya bar wurin aikinsa ba tare da sanin hukuma ba, ya ce mahaifiyarsa mayya ce shiyasa ya kasheta Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta damke wani soja mai mukamin Kofur mai suna Charles Thompson a kan zarginsa da ake da sokawa mahaifiyarsa mai suna Modupe Thompson wuka sau babu adadi har ta rasu a aranar talata, 29 ga watan Disamba.
Charles wanda ya saba dukan mahaifiyarsa a kowanne fada da ya hada su ya soka mata wuka sannan ya tsere.
Rundunar 'yan sandan ta damke shi a ranar Talata, 31 ga watan Disamba, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
A yayin zantawa da manema labarai, Charles ya tabbatar da cewa ya kashe mahaifiyarsa saboda mayya ce.
"An kama ni sakamakon laifin kisan kai da nayi. Mahaifiyata ta mutu a hannuna yayin da muke fada. Na sha ganinta tana komawa jemage da dare, lamarin da ke ci min tuwo a kwarya.
"Tana bayyana kuma ta bace. A lokacin da na shiga daki na ganta da yaro mai shekaru 10. Hakan ne yasa muka fara fadan," yace. Charles ya yi ikirarin cewa ya dauka hutu ne saboda bashi da lafiya amma bincike ya nuna cewa barin wurin aiki yayi.
"A halin yanzu na dauka hutu ne saboda bani da lafiya. Na fadi ne yayin wani hari da aka kawo mana a Maiduguri. Ba a kore ni daga aiki ba," yace.
Thompson wanda yace mahaifinsa ya bar mahaifiyarsa tare da sauran 'yan uwansa sama da shekaru 20, ya zargi cewa mahaifiyarsa bata taba sonsa ba.
'Yan sanda sun tabbatar da cewa za su kai shi kotu bayan sun kammala bincike.
Source: Legit
0 Response to "Na halaka mahaifiyata ne saboda mayya ce, Sojan da ya tsere daga wurin aiki "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?