
Mun gaji da jira: Mazan Hausawa su rinƙa auren mata fiye da 1, budurwa ta koka
Wata matashiyar budurwa daga arewa ta gaji da zaman gwauranci don haka ta je shafin soshiyal midiya don yin magana
Budurwa mai shafin Twitter @3yesharu ta yi kira ga mazan Hausawa da suka yi aure fiye da shekaru biyar a kan su duba yiwuwar karin aure
A cewarta, layin yan matan da ke jira a dauke su a matsayin matan aure na biyu ya dade da cika
Wata matashiyar budurwa mai shafin Twitter @3yesharu ta yi kira ga mazan Hausawa magidanta a kan su duba yiwuwar yin karin aure, cewa yan mata da ke kan layi sun gaji da jira.
Matashiyar wacce ta fito daga yankin arewacin kasar ta yi kiran ne ga mazan Hausawa da suka yi aure fiye da shekaru biyar da suka gabata.
Ta wallafa a shafinta na Twitter:
“Mazan arewa da suka yi aure tsawon shekaru 5+ ina ganin lokaci yayi da za ku fara kallonmu yan rukunin B. Mun isa a kwashemu amma layin baya tafiya.”
Yan Najeriya sun je bangaren yin sharhi a karkashin rubutunta don bayyana ra’ayinsu
Arewa men that have been married for 5+ years I think it's time you start looking at us in Batch B. We are due for recruitment but the line is not moving.
— Matar Alhaji 💅🏾 (@3yesharu) December 5, 2020
Shafin @mbkusharki ta wallafa:
“Abun bakin ciki rukunin A sun daga ginshiki mai inganci ta yadda yiwuwar shigowar rukunin B na a kusa da 0%.”
@olahassan ya rubuta:
"Dole sai mazan Arewa? Wasun mu daga kudu maso yamma mun fi dacewa. Ki tambayi kawayenki da suka yi aure daga wannan yanki na Naija yadda muke da dadin zama.”
@deendeenoo ta wallafa:
"Wallahi kin fadi zukatan yan mata da dama. Amma soshiyal midiya ya sauya tunanin maza a yanzu saboda wasu mata da dama suna kokarin yin rayuwa sabanin wanda addini da al’ada suka koyar dasu. Maza na gudun mata masu aikata hakan.”
@mustaphahodio ya rubuta:
“Da sai ki yi kira ga yan uwanki mata a Batch A don su barmu mu kwashi yan Batch B.”
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Mun gaji da jira: Mazan Hausawa su rinƙa auren mata fiye da 1, budurwa ta koka"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?