Matata ta tare da wani namiji a barikin mu, sojan mai ritaya ya shaidawa kotu
Wani sojan sama mai murabus ya roki wata kotu da ta raba auren shi da matarsa da yace ta hana shi ganin yayansa
Ya kuma shaidawa kotu cewa matar ta tare da wani namijin daban bayan da shi ya tafi Borno aiki tare da kai karamin dansu wajen mahaifiyarta ba tare da izininsa ba
Matar ta musanta zargin, kuma ta ce shi ne baya turo musu kudin abinci shiyasa ta kaisu kauye ta kuma tare a gidan kawar ta saboda albashinta ba zai isa ita da yara ba
Wani sojan sama mai ritaya dan shekara 39, Richard Imana ya roki wata kotun gargajiya a Iyana-Ipaja da ke jihar Lagos da ta raba aurensa, saboda wulakanta shi da hana shi ganin yayansa da matar sa ke yi.
Richard ya shaidawa kotu cewa matarsa, Nkem, ta bar gidan auren ta, ta kuma bi wani mutumin a barikin da ya ke zaune da iyalansa. Ya ce matar ta koma wajen mutumin lokacin da shi ya ke aiki a Borno, Vanguard ta ruwaito.
"Matata ta rufe bangare na, ta tare a gidan wani lokacin ina Borno. Ta guje ni saboda wani, nayi murabus don kula da yayanmu.
"Akwai lokacin da bani da lafiya likita ya bukaci ta sanya hannu a takardu don ayi min magani amma ta ƙi. " Ta hana ni ganin yara na, ta dauke karamin ta kaiwa mahaifiyar ta ba tare da izini na ba," a cewar mai karar.
Da take maida martani, Nkem mai shekara 34 ta ce ita fa ba wajen wanda ta koma, ta je wajen kawarta ne wadda ta ke makwabciyar ta saboda mijin ta ya daina tura mata kudin abinci.
"Na kai yaya na kauye lokacin da hakan ke faruwa saboda mahaifinsu baya turo kudin abincin su. "Na kwashe kaya na cikin fushi, saboda lokacin, albashi na N25, 000 kuma bazai isa ni da yara ba," a nata jawabin.
Ta ce ya shigar da karar ne a bisa rashin fahimta. Sai dai duk ma'auratan biyu sun bayyana cewa har yanzu su na kaunar junansu sai dai kawai rashin samun lokacin tattaunawa.
Alkalin kotun, Prince Adewale Adegoke ya gargadi Nkem kan tarewa tare da kawar ta. Ya kuma umarci a dawo da karamin dan su Lagos a kuma hada shi da baban shi. Adegoke ya ce su zauna lafiya ya kuma dage cigaba da sauraron ƙarar zuwa 15 ga Disamba don daukar mataki.
SOURCE: LEGIT
0 Response to " Matata ta tare da wani namiji a barikin mu, sojan mai ritaya ya shaidawa kotu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?