
Matashiya sanye da hijabi ta wallafa hotunanta, ta nemi sanin ko da gaske tana kama da Nicki Minaj
Ana ta cece-kuce kan hotunan wata matashiya sanye da hijabi wacce ta wallafa hotunanta a kan Twitter, tana tambayar ko tana kama da Nicki Minaj - Mutane da dama na kallon hakan a matsayin cin mutuncin addininta tunda har za ta iya yin wannan kwatanci da mawakiyar ta Amurka
Akwai kuma mutanen da suka kasa gane abunda ya fusata mutane game da matashiyar wacce ta wallafa kyawawan hotunanta a yanar gizo Wata matashiya yar Najeriya mai suna @Hafsaat_mohd a shafin Twitter ta wallafa hotunanta sanye da hijabi a yanar gizo, inda ta tambayi mutane ko tayi kama da mawakiyar Amurka Nicki Minaj.
Yayinda wasu suka yaba da kyawunta, wasu sun je karkashin hotunanta domin caccakar kwantancin da tayi, cewa mace mai mutunci ba za ta hada kanta da mutum da baida mutunci ba. Akwai kuma wasu da suka ce ta fi mawakiyar kyau. Hotunan nata ya tattara dubban sharhi daga mutane.
Kalli wallafar tata a kasa:
Is it true i look like nicki minaj?🤔❤ pic.twitter.com/LCY2Adped3
— Hafsaah🌻 (@Hafsaat_mohd) December 3, 2020
Ga wasu daga cikin sharhin:
@al_muhammadu yace: “Ina sa ran za ki fusata idan wani ya fada maki cewa kina kama da Nicki Minaj, a wajena hakan cin mutunci ne sosai gaskiya kada ki kwatanta kanki da irin wannan matar.”
@Farouqaadam1 yace: "Subhanal_Lah, baki yi kama da ita ba. Dan Allah ki yi watsi da wannan Kalmar, ke Musulma ce, kin fita sosai; kamar tazarar da ke tsakanin sammai da kassai.”
@goodconstantine ya ce: "Zancen gaskiya. Ki so ki yi kama da ita. Ina son Nicki amma an yi aiki sosai kafin ta kai yadda take a yau.”
@Red_negro_ yace: "Lmao. Na bude fagen sharhi don yabawa da kyawun yarinyar nan kawai sai naga mutane suna nuna kiyayya kan matar da ta fi ahlinsu gaba daya.”
@MosesRhyris tace: "Dukkanin mutanen nan da ke cewa kada ta kwatanta kanta da ita za ka same su da wakokin Nicki Minaj dankare a wayoyinsu...munafirci.”
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Matashiya sanye da hijabi ta wallafa hotunanta, ta nemi sanin ko da gaske tana kama da Nicki Minaj "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?