Masari ya bayyana yawan yara 'yan makaranta da ke hannun 'yan bindiga
Sunday, 13 December 2020
Comment
Gwamnan jihar Katsina ya ce yanzu haka ana neman dalibai 333 na makarantar sakandaren Kankara, an samu nasarar ceto sauran
Ya ce suna bukatar duk iyayen da yaransu suka koma gidajensu su sanar da hukuma don a san yawan wadanda aka yi garkuwa dasu
Ya sanar da hakan ne lokacin da ministan tsaro da sauran manyan ma'aikatan tsaro suka je Katsina yi masa jaje a ranar Lahadi A ranar Lahadi gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce har yanzu ba a ga dalibai 333 ba na makarantar sakandare ta kimiyya da ke Kankara, Punch ta wallafa.
Ya bayyana hakan lokacin da ministan tsaro, janar Salihi Magashi, ya jagoranci shugabannin tsaro zuwa jihar Katsina don yi wa gwamnan jaje a kan satar daliban makarantar sakandare da aka yi ranar Juma'a a jihar Katsina.
Wadanda suka kai ziyarar sun hada da shugaban jami'an tsaro, shugaban sojojin sama da sauransu
Gwamnan ya ce, "Tabbas an ketare jihar da yaran da aka sata daga wuraren kwanansu, saboda akwai yara daga jihohi daban-daban a makarantar.
"Gabadaya daliban guda 839 ne, yanzu muna binciken inda dalibai 333 suke. Har yanzu muna cigaba da gano inda suke, sannan muna kira ga iyaye da su kira kuma su sanar damu idan sun koma gidajensu.
"A yadda labarai suka iso mana, har yanzu ba a ga dalibai 333 ba, muna ta binciken dazuzzukan, sannan muna neman iyayen daliban ko yaran sun gudo gida don mu san yawan daliban da aka yi garkuwa dasu."
Masari ya ce har yanzu masu garkuwa da mutanen basu kira gwamnati ko kuma wani ba dangane da amsar kudin fansa ba. Ya tabbatar da yadda suka yi iyakar kokarinsu wurin ceto daliban.
Janar Magashi ya tabbatar wa da gwamnan jihar cewa za su bayar da gudunmawa kwarai.
SOURCE: LEGIT
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Masari ya bayyana yawan yara 'yan makaranta da ke hannun 'yan bindiga"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?