--
Maryam Sanda: Dalilai 3 da suka sa kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa

Maryam Sanda: Dalilai 3 da suka sa kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa

Alkalin kotun da Maryam sanda ta daukaka kara ya tsaya a kan tsohon hukuncin da aka yanke wa Maryam - Ya tsaya a kan hukuncin da aka yanke mata ne bisa wasu kebabbun dalilai gamsassu guda uku 


Alkalin ya ce ya gamsu ita tayi kisan, sannan babu wani dalili da zai sa ta watsar da tsohon hukuncin Daukaka karar da Maryam Sanda tayi na babbar kotu, a kan kisan mijinta da ake zargin ta yi a ranar Juma'a, 4 ga watan Disamba, shi ya fara janyo cece-kuce a Najeriya. 


Kwamitin bincike na mutum 3, wanda Alkali Stephen Ada ya jagoranta, ta kori daukaka karar Sanda a ranar Juma'a. Idan ba a manta ba, ana zargin Sanda da kashe mijinta, Bilyaminu Bello, wanda da ne ga dan uwan tsohon shugaban jam'iyyar PDP. 


Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar Litinin, 27 ga watan Janairu, bayan 'yan sanda sun kama ta dumu-dumu da laifin kisa a watan Nuwamban 2017. 


Alkali Yusuf Halilu ya ce akwai duk wasu shaidu da ake nema, wadanda suka tabbatar da cewa Maryam Sanda ce ta kashe mijinta, garin dambensu ya fada kan tukunyar shisha ya mutu. Bayan hukuncin ya janyo cece-kuce, Legit.ng ta bayyana dalilai 3 da suka sanya Alkali Halliru ya yanke mata hukuncin sakamakon yadda kwamitin binciken mutum 3 suka tabbatar da hakan. 



1. Rashin iya maganar Sanda yayin daukaka karar, da kuma nuna lallai sai kotu ta jingine shari'ar da ta gabata, inda Sanda tace ba a yi mata adalci ba. A cewarta, Alkalin ya nuna son kai, duk da duk wasu shaidu da ake nema duk an samu. 


An yanke hukuncin ne bayan an samu shaidu kwarara, rashin magana mai dadi ga kotu, boye makamin da aka yi amfani dashi wurin kisan, sabawar maganganun shaidunta da kuma kin bayyana gaskiyar abinda ya janyo mutuwar mijinta. 


2. Kamar yadda alkalin yace a ranar Jama'ar da ya yanke hukunci, babu dalilin da zai sa a share hukuncin da waccan kotun tayi, a yi wani daban. Baya ga rashin nagartar Sanda, duk wasu shaidu da ake nema sun bayyana karara, wadanda suke nuna cewa ita ce take da laifi. Don haka dole ne kotu tayi adalci, babu wani rangwame.


3. Sanda ta kasa tabbatar wa da kotu cewa fasassar tukunyar shisha ce tayi ajalin mijinta. Duk da ta tsaya tsayin-daka a kan cewa abinda yayi ajalin mijin nata kenan, kwamitin binciken mutum-3 tace maganar kanzon kurege ce. Alkalin ya ce hujjar Sanda ta yi kadan da ta gamsar da kotu cewa ba da gangan aka yi kisan ba. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Maryam Sanda: Dalilai 3 da suka sa kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin kisa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?