Kwankwaso ƙaryata Ganduje, ya sanar da ainihin dalilin da yasa ya naɗa Sanusi a Kano
Thursday, 24 December 2020
Comment
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje martani kan batun nada Sanusi II sarkin Kano
Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ya nada Sanusi sarki ne domin cin zarafin Goodluck Jonathan
Kwankwaso ya ce ya bi doka wurin nada Sanusi II kuma ya zabe shi ne don ya fi sauran maneman ilimin addini da boko,
ya kuma fi karbuwa wurin al'umma Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi'u Kwankwaso ya musanta zargin nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano don cin zarafin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Ya yi wannan jawabi ne yana mai mayar da martani ga zargin da Gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje ya yi masa, The Nation ta ruwaito.
Ganduje ya yi wannan zargin ne a wurin bikin kaddamar da wata littafi. Ya kuma kara da cewar ko lokacin da a ka nada Sanusi a 2014, ba shi ne mafi cancanta ba. Ya kuma ce an tsige Sanusi ne don kare martabar masarautar .
Sai kuma ga shi Kwankwaso ya fito ya musanta hakan ya na mai cewar an bi ka'idar masarautar Kano yadda ya kamata wurin nadin Sanusi.
Ya ce Sanusi ya fi sauran maneman ilimin Boko da Addini kuma ya fi su karbuwa wurin jama'a.
"Matsuwar da Gwamna Ganduje ya yi na neman ciwo bashin dala biliyan 1.8 da kuma Allah wadai da Sanusi ya yi game da hakan shi ne dalilin tsige shi.
"Kowa ya san Sanusi ya fi Ganduje wayewa wanda wannan shi ne dalilin tsige shi da kuma kacaccala masarautar da kuma nada Sarakunan da za su biyema son ransa," In ji Kwanjwaso ta bakin babban sakatarensa.
Source: Legit
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Kwankwaso ƙaryata Ganduje, ya sanar da ainihin dalilin da yasa ya naɗa Sanusi a Kano"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?