Korona ta harbi sabbin mutane 758 a Nigeria, fiye da mutum 100 a Kaduna
Tuesday, 15 December 2020
Comment
Alamu na nuni da cewa da gaske annobar korona ta sake yunkurowa a karo na biyu - Alkaluman masu kamuwa da kwayar cutar sai kara hawan gwauron zabi suke yi a 'yan kwanakin baya bayan nan
Tuni Jihohi suka fara bayar da umarnin rufe makarantu, musamman na Firamare da Sakandire Alkaluman baya bayan nan akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria suna saka damuwa a zukatan jama'a tare da fargabar cewa za'a koma gidan jiya.
Mutane 758 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Talata, 15 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.
Sanarwar ta nuna cewa alkaluman wadanda suka kamu da kwayar cutar a babban birnin tarayya, Abuja, sun ninka adadin wadanda kwayar cutar ta harba a jihar Legas.
Daga jihar Kaduna, mutane 103 ne sakamakon gwajinsu ya nuna cewa suna dauke da kwayar cutar.
Ga jerin jihohin da adadin mutanen da suka kamu da kwayar cutar a jihohin da sunayensu suka bayyana a sanarwar NCDC ta daren ranar Talata.
Jimillar sabbin mutane 758 sun kamu da kwayar cutar #COVID19 a Nigeria; FCT-305 Lagos-152 Kaduna-103 Bauchi-44 Gombe-35 Plateau-31 Rivers-17 Sokoto-15 Kwara-13 Kano-9 Ebonyi-8 Ogun-5 Osun-5 Oyo-4 Edo-4 Anambra-4 Bayelsa-2 Ekiti-1 Taraba-1
758 new cases of #COVID19Nigeria;
— NCDC (@NCDCgov) December 15, 2020
FCT-305
Lagos-152
Kaduna-103
Bauchi-44
Gombe-35
Plateau-31
Rivers-17
Sokoto-15
Kwara-13
Kano-9
Ebonyi-8
Ogun-5
Osun-5
Oyo-4
Edo-4
Anambra-4
Bayelsa-2
Ekiti-1
Taraba-1
74,132 confirmed
66,494 discharged
1,200 deaths pic.twitter.com/gkdRmj8HXp
SOURCE: LEGIT
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Korona ta harbi sabbin mutane 758 a Nigeria, fiye da mutum 100 a Kaduna"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?