--
Karya ne, bamu baiwa Ganduje Farfesa ba, jami'ar East Carolina

Karya ne, bamu baiwa Ganduje Farfesa ba, jami'ar East Carolina


Jami'ar ECU ta ce Malammin da ya baiwa Ganduje matsayin Farfesa aikin gabansa yayi - Sakataren yada labaran Ganduje ya sanar da an baiwa Ganduje gurbin aiki a jami'ar Wata jami'ar kasar Amurka, East Carolina ECU, ta karyata nada gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin Farfesa mai ziyara.


Jaridar Premium Times ta aike wasika jami'ar ranar Alhamis domin tabbatar da sihhancin labarin nadin Ganduje duk da cewa an kama shi a bidiyo yana karban daloli. A martanin jami'ar, ta bayyana ainihin abinda aka aikewa Ganduje. Mukaddashin shugaban jami'ar, Grant Hayes, ne ya rattafa hannu kan wasikar. Wasikar yace: 


"Na samu labarin cewa ka samu wasika daga daya cikin mambobin tsangayar mu a ranar 30 ga Nuwamba, 2020, cewa an baka gurbin aiki a cibiyar cigaban ilmin zamani a tsangayar ilmin kasuwanci na jami'ar East Carolina." 


"Ina son sanar da kai cewa wasikar da ka samu daga Dr. Victor Mbarika, ranar 30 ga Nuwamba, bai zo da wani matsayi na gurbin aiki ko nadi matsayin Farfesa daga hukumomin jam'iyar East Carolina ba." "Cansala kadai, Ni, ko wani sanannan jami'i a sashen karatu zai iya sanya hannu kan takardan bada gurbin aiki. Dr Mbarika bai da irin wannan izini," wasikar ya kara. 


Zaku tuna cewa sakataren yada labarin Ganduje, Abba Anwar, a jawabin da ya saki ranar Talata cewa cibiyar bunkasa fasahar sarrafa labarai ta kasa da kasa a Jami'ar East Carolina da ke kasar Amurka, ta dauki gwamnan jihar Kano, 


Dakta Abdullahi Umar Ganduje, aiki a matsayin Lakcara. Jami'ar ta ce ta zabi karrama Ganduje da wannan aiki ne domin samun damar karuwa da dumbin iliminsa, basirarsa, da kwarewa a harkar mulki. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "Karya ne, bamu baiwa Ganduje Farfesa ba, jami'ar East Carolina"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?