--
Karuwar yawan masu HIV a Najeriya: UNFPA ta bayyana wadanda abun ya fi shafa

Karuwar yawan masu HIV a Najeriya: UNFPA ta bayyana wadanda abun ya fi shafa


A ranar Talata, UNFPA ta ce kashi 50 bisa 100 na masu HIV karuwai ne da 'yan luwadi - A cewarta, dole ne duk mai kanjamau ya kiyaye kansa daga COVID-19 don za ta iya ajalinsa - Darektan UNFPA, Dr Natalia Kanem ce ta shaida hakan a Abuja, a ranar kanjamau ta duniya 


A ranar Talata, UNFPA tace kashi 50 bisa 100 cikin wadanda basu dade da samun kanjamau ba, karuwai ne da 'yan luwadi. Sai dai ta yi takaicin sanar da cewa kaso kadan ne daga kudaden da aka ware don shawo kan HIV za a sadaukar garesu, jaridar Vanguard ta tabbatar. 


UNFPA ta bayyana hakan a wata takarda wacce darektan ta, Dr Natalia Kanem ta gabatar a Abuja ta zagayowar ranar kanjamau ta duniya ta shekarar 2020, wacce tayi wa take da, "Kawo karshen cutar HIV/AIDS: Janyo masu cutar a jiki, da kwantar musu da hankali."


UN ta bayyana yadda masu HIV za su fi saurin kamuwa da cutar COVID-19 kuma ta illata su. Kanem ta ce mafi yawan wadanda suke samun cutar HIV a fadin duniya, karuwai ne da kuma maza 'yan luwadi. Suna samun cutar ne sakamakon yin jima'i da mutane daban-daban. 


"Alamu sun nuna cewa babban hatsarin da masu HIV za su fuskanta shine idan suka kamu da COVID-19 don hakan zai iya sanadiyyar mutuwarsu cikin kankanin lokaci." A cewarta, matsawar ana son kawo karshen HIV, wajibi ne a dinga janyo masu cutar a jiki. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


Related Posts

0 Response to "Karuwar yawan masu HIV a Najeriya: UNFPA ta bayyana wadanda abun ya fi shafa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?