
Kar ku saki jiki, har yanzu akwai Korona, ko jiya Alhamis mutane 343 suka kamu -NCDC
Da alamun mutane sun fara sakin jiki kan lamarin annobar Korona duk da cewa daruruwan yan Najeriya na sake kamuwa da cutar kulli yaumin
Gwamnatin tarayya ta shawarci masu shirye-shiryen bikin Kirismeti su bi hankali
Hukumar NCDC ta bayyana adadin wadanda suka kamu da cutar ranar Alhamis a fadin tarayya Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 343 ranar Alhamis a cewar alkaluman hukumar kiwon lafiya, NCDC.
Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 68,303 a Najeriya.
Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Alhamis , 4 ga watan Disamba, 2020. Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.
Daga cikin mutane sama da 68,000 da suka kamu, an sallami 64,291 yayinda 1179 suka rigamu gidan gaskiya.
Ga jerin adadin wadanda suka kamu a jihohin Najeriya:
FCT-123 Lagos-106 Kaduna-72 Nasarawa-14
Rivers-5 Bauchi-4 Imo-4 Ogun-4 Ekiti-3 Edo-2 Oyo-2 Plateau-2 Akwa Ibom-1 Kano-1
Ga jerin jiha-jiha:
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Kar ku saki jiki, har yanzu akwai Korona, ko jiya Alhamis mutane 343 suka kamu -NCDC"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?