--
Kano: APC da PDP sun fara musayar yawu a kan zaben kujerar gwmna a 2023

Kano: APC da PDP sun fara musayar yawu a kan zaben kujerar gwmna a 2023




Har yanzu da sauran shekaru biyu masu kwari kafin gudanar da zabukan shekarar 2023 


yana cewa ba za ta sake yarda da salon zaben 'Inconclusive' ba, APC ta ce za ta murde zaben baki daya A jihar Kano, 


jam'iyya mai mulki APC da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP sun fara cacar baki musayar yawu akan zaɓen gwamna mai zuwa na shekarar 2023,kamar yadda Vanguard ta rawaito. 


Jam'iyyar PDP, a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ta ce ba za ta lamunci duk wani wargi a zaɓen gwamna mai zuwa da sunan 'Inconclusive', watau zaben da bai kammalu, ba. 


Ita kuwa jam'iyya mai mulki, APC, a ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Abbas, ta sha alwashin sake maimaita wani 'Inconclusive' din tare da tafka maguɗi a kakar zaɓen shekarar 2023 mai zuwa. 


Abbas, ya yi wannan furucin ne, a matsayin mayar da martani ga kalaman tsohon gwamna Kwankwaso, lokacin rantsar da sabbin shugabannin jam'iyyar APC a gidan gwamnatin Kano a yammacin ranar Talatar. 


Abdullahi Abbas ya ce, "Kwankwaso ya sha alwashin zaɓe mai zuwa sai dai a mutu ko a yi rai, to ba damuwa, muna shirye da hakan mu ma. Ai mu ba matsorata ba ne. Mun shiryawa yaƙin. Ba ma tsoron a mutu.


"Magoya bayan jam'iyyarmu, kar ku ragawa Kwankwaso shi da magoya bayansa. Idan suka zage ku a radiyo ko a waje, kar ku raga musu. 


"Kai bari na gaya muku gaskiya, sai ma mun murde zaben 2023 kuma babu abinda zai faru. Za mu nunka abinda mu ka yi a mazabar Gama babu abinda aka isa a yi. Wannan lokacinmu ne. Gwamnatinmu ce." In ji Abdullahi Abbas shugaban jam'iyyar APC. 

 Source: Legit 


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Kano: APC da PDP sun fara musayar yawu a kan zaben kujerar gwmna a 2023"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?