Kalli Yadda wasu yara suka tuttule jarkan mai kacokan a kan motar iyayensu
Wednesday, 23 December 2020
Comment
Wata fusatacciyar uwa, Bongiwe Malunga, ta wallafa hotunan kananan yaranta da motar da suka lalata
Bongiwe ta bayyana cewa za ta hukunta su ta hanyar soke kayan sabbin kayan kirisimetinsu
Mabiya shafin Twitter sun yi sharhi kan wallafarta yayinda wasu suka nemi a sanya idanu sosai a kan yaran a koda yaushe Duk da kasancewar yara abun sha’awa mafi akasarin lokuta sun iya barna idan ba a lura dasu ba.
Wata uwa mai suna Bongiwe Malunga ta je shafin Twitter don nuna barnar da yaranta suka yi. A wasu jerin hotuna da ta wallafa a yanar gizo, an gano yaran tsaye a gefen motan da jarkan mai. A matsayin hukunci, matar ta bayyana cewa ba za ta yi wa yaran kayan bikin Kirsmeti ba.
Hotunansu ya janyo cece-kuce sosai daga iyaye da mutane a yanar gizo. Kalli wallafarta a kasa:
No Christmas cloths for these 2 pic.twitter.com/VRs3Aty3AH
— Bongiwe Malunga (@BIndlovukazi) December 19, 2020
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, wallafar mahaifiyar ya samu fiye da likes 40,000 da dubban sharhi. Kamara Yanda Jaridar Legit.ng ta tattaro wasu sharhi a kasa:
@SkedoKimZ ya ce: “Kalle su kamar na kwarai yayinda suke ci gaba da tsayuwa a wajen aika-aikan da suka yi.”
@Observer_July ya ce: “Amma fa laifinki ne na rashin adana man ta yadda ba za su gani ba. Toh da ace sun sha ne fa? Ko kuma su samu hanyar cinna masa wuta sannan su kona kansu?”
@Boipelo_Joy tayi martani: “Yara sun wuce tunanin mutum kuma duk taka-tsan-tsan da mutum zai yi a koda yaushe suna da aika-aikan da za su yi."
Source: Legit
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Kalli Yadda wasu yara suka tuttule jarkan mai kacokan a kan motar iyayensu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?