
Kalli Hotunan wani Yanki A jihar Adamawa inda jama'a ke shan ruwa daya da dabbobinsu
Mazauna yankin, yayinda suke korafi, sun bukaci a kawo masu dauki saboda suna tunanin an manta da su Folwoya Goriji, wani garin manoma a yankin Ndikong da ke karamar hukumar Mayo Belwa na jihar Adamawa, na da hanyar samun ruwa guda daya ne tal.
Al’umman kauyen na rokon gwamnatocin jiha da na kananan hukumomi su share masu hawayensu daga illar da ke tattare da shan ruwa a waje guda da dabbobinsu.
An kawo Baba Musa, wani mazaunin kauyen, ya na fadin cewa: “A lokacin yakin neman zabe ne kawai muke ganinsu (yan siyasa) tare da alkawaransu na bogi da karya. Don Allah, kalli ruwan da muke sha tare da dabbobinmu kamar an manta da mu.
Ya ce: “Ruwan sha mai inganci, gyara da tsafta na daga cikin hanyoyi biyar na dakile cututtuka. “Saboda haka yana da muhimmanci zababbun shugabanninmu su samar da ruwa mai inganci, da tabbatar da tsaftar muhalli da na jiki a yankunan karkara.
Legit.ng ta yi kokarin samun kansila da ke wakiltan yankin amma abun ya ci tura domin an ce baya gari. Yunkurin jin ta bakin Shugaban karamar hukumar ma bai haifar da yaya masu idanu ba.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Kalli Hotunan wani Yanki A jihar Adamawa inda jama'a ke shan ruwa daya da dabbobinsu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?