
Kalli Hotunan dankareriyar doya da aka girbe a Anambra wacce ta mamaye mota daya
Wani mutum mai suna Osita Amakeze, ya wallafa hotunan wata dankareriyar doya a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba wacce yace an nomata a kauyen Agulu, jihar Anambra. A cewarsa, wannan doyar suke kira "ofu ji a ne-eme offload".
Bayan ya wallafa hotunan doyar ne mutane da dama suka yi ta mamaki, kuma suna yaba wa girman doyar. Dama a shekarar da ta gabata, ya wallafa hotunan wata doya wacce yace abokinsa ne ya noma ta. A cewarsa, doyar tana da nauyin 153.10 kuma duk kauyen su babu doya mai girmanta.
Mutane da dama sun yi ta tsokaci iri-iri a kan doyar, har wani Izuchuxy yana cewa: "Menene sirrin? Wacce iriyar doya ce wannan? Mutane nawa ne suka taimaka wurin nomata? A gaskiya wannan dankareriyar doya ce."
Wani Chabalus16 ya ce: "Wannan daya ne daga cikin abubuwan da nafi so idan nayi tafiya kauye don shagalin kirsimeti. Har na kosa inje in taya kakata hako doyarta."
#Agulu bụ Ijele, 2019
— . (@OsitaAmakeze) September 6, 2019
So, Nkaonadi's Obeagu gigantic #yam weighs 153.10 to beat every other. Competition continues at Anịocha. If it comes 1st the entire LG, it goes to the #State Ekwueme Square @WillieMObiano.
Meanwhile, Nkịtaku's Chief Ezisi donates buses to winners#pic2017 pic.twitter.com/GjOJ6S7q11
So, today I went to #Agulu to see the monstrous yam of my good friend, Nkaonadi of Obeagụ. This yam tuber is the type my people refer to as, "ofu ji a na-eme offload." You see where it was unearthed and another grave dug already to entomb great harvest of next year. #iheakụakụ pic.twitter.com/4w3dvMNQer
— . (@OsitaAmakeze) December 2, 2020
Wani ccebuka kuwa cewa yayi: "Ban taba ganin katuwar doya irin wannan ba. Don Allah, menene sirrin?"
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Kalli Hotunan dankareriyar doya da aka girbe a Anambra wacce ta mamaye mota daya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?