
(Kalli bidiyon) Ango ya fusata bayan amarya ta cinye abincin da aka tanada don shi a wajen liyafar aurensu
An gano wani ango da ke cika yana batsewa a wajen liyafar bikinsa bayan abunda amaryarsa tayi - Ya kamata amaryar ta ciyar da sabon angon nata abinci amma maimakon haka sai ta ambada a nata bakin
An gano bakin da suka halarcin taron suna yi wa ma’auratan dariya An gano bidiyon wata amarya da ango kwanan nan a shafin soshiyal midiya kuma ya samu martani na ban dariya daga yan Najeriya. Bidiyon ya nuno wasu ma’aurata a wajen liyafar aurensu.
Da aka kai lokacin ciyar da ango sai aka gano sabuwar amaryar ta tsuguna kan gwiwowinta yayinda shi kuma angon ya zauna kan wani kayataccen kujera fari. Kyakyawar amaryar, wacce ke sanye da kaya launin ja, ta dibi abinci a hannunta don ciyar da angonta.
Sai dai kuma, da lokacin zubawa mijin abinci a bakinsa yayi inda ya riga ya bude shi, sai amaryar tayi saurin janye hannunta sannan maimakon haka sai ta zuba a nata bakin.
Abunda amaryar tayi ya fusata angon nata sannan wata bakuwa a bayan angon ta kara tunzura lamarin ta hanyar yi masa dariya.
Kalli bidiyon ban dariyar a kasa:
Martanin yan Najeriya game da bidiyon: kambeaut.y:
“Ya yi kaman zai mangareta, amma ya kasa saboda taron jama’a.” naijaplayboi: “Na rantse wannan gayen zai dunga dukan mata. Kalli jijiyoyin kansa yadda suka fito cikin kasa da sakan biyu.”
imagobelle: “Irin wannan miji da bai san wasa ba ehn.” amyk_8890: “Kalli fusataccen fuskarsa, kilan da ba a bainar jama’a bane da ya waska mata mari daya.”
SOURCE: LEGIT
0 Response to " (Kalli bidiyon) Ango ya fusata bayan amarya ta cinye abincin da aka tanada don shi a wajen liyafar aurensu"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?