--
banner
Kafin ka nemi auren ƙabilar Ebira: Muhimman abubuwan da ya kamata ka sani

Kafin ka nemi auren ƙabilar Ebira: Muhimman abubuwan da ya kamata ka sani





Kabilar Ebira ana samun su ne a jihar Kogi musamman a kananan hukumomi biyar na jihar da suka hada da Okehi, Ajaokuta, Okene, Ogorimagongo da Adavi. Baya ga jihar Kogi, kabilar sun yadu a fadin wasu jihohin Najeriya musamman a Ondo da Ekiti. 


Matan kabilar sun kasance masu tsantsar kyawu kuma cikin sauki hankalin maza ke karkata a kansu. Kyawunsu kadai zai sa mutum ya ji yana kaunarsu a ganin farko.


Sai dai duk da kyawunsu akwai abubuwan da ya kamata ka sani game da su kafin ka auresu. Dalili kuwa shine domin ka shirya kan abunda za a nema daga gareka a lokacin bikin. 


Ga wasu daga cikin abubuwan: 

1. Mafi akasarin mutanen kabilar Musulmai ne wanda hakan ke nufin yawancin kyawawan yan Ebira da kake gani Musulmai ne wadanda suka riki addini sosai, kuma da wuya a sauya su ta dalilin aure. 


2. Idan kana son aure daga kabilar Ebira, ba huruminka bane sanar da iyayenta kudirinka. Yayinda wasu da dama ke tunkarar iyayen yarinya kai tsaye don sanar masu da kudirinsu, a al’adar Ebira, magabatanka ne za su aikata hakan. 


3. A yayin baiko wanda ake kira da ‘Ise Ewere’ da yaren Ebira, magabatansa ne za su je gidan surukansu don yin wasu al’ada. 


Sannan a yayin baikon, magabatan amaryar za su samar da kayan abinci da na sha domin karrama bakinsu. 


A yayin baikon kuma, magabatan angon za su samar da wasu kayayyaki kamar haka: 

Doya guda 100 Bushasshen kifi da naman daji Lemukan sha Goro Man ja Buhun gishiri Man gyada Sarkoki na amarya Tufafin sawa a cikin jaka na amarya Zanuwa biyu na amarya (ba dole bane) Kudi na magabata Wasu daga cikin wadannan kayayyaki ba dole bane bisa ga al’ada saboda ya danganta da ra’ayin yan uwan amaryan. 


Idan suka ga dama suna iya soke kayayyakin. Wani abu kuma da za a lura game da kayayyakin shine, ana raba mafi akasarinsu ne ga yan uwa da makwabta domin su sanyawa amaren albarka. 


4. Kudin sadaki Magabatan amarya ne ke yanke kudin sadaki kuma mafi yawan lokuta su kan duba karfi da wadatan angon ne. Sai dai kuma akwai wasu kudade da wajibi ne a biya su bisa ga al’ada, kamar: 

1. OZEMEIYI: Wannan kudi ne da ake biya don tabbatar da cewar angon na muradin amaryar. 

2. OTANUVOGE: Wannan shine kudin da ake biya domin hada hannayen ma’auratan a waje daya.

3. IDOZA: A lokutan baya, mutumin da ke son auren yarinya dole ya taimakawa surukansa a gona amma a yanzu, kudi ake biya a madadin haka. Kudin da za a biya saboda haka shine Idoza. Mun samu wannan cikakken bayani ne a wani wallafa da shafin Arewa RantHQ yayi a Facebook.


Source: Legit 


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Kafin ka nemi auren ƙabilar Ebira: Muhimman abubuwan da ya kamata ka sani"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?