Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta shiga cikin jerin mutanen da suka fi tashe a intanet a 2020
Rahama Sadau ta yi nasarar shiga cikin jerin mutanen da suka fi tashe a yanar gizo a 2020 - Ko shakka babu jarumar ta Kannywood ta samu shiga wannan rukuni ne saboda rigimar da ta fada bayan bayyanar wasu hotunanta
Ta kuma shiga jerin mutanen da aka fi neman karin haske a kansu a shafin Google a Najeriya a shekarar 2020 Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Rahama Sadau, ta shiga sahun yan Najeriya da suka fi tashe a shafin yanar gizo cikin shekarar 2020.
Rahama ta kasance ta hudu a cikin wannan rukuni na mutanen da suka tashe a shafin na intanet a kasar, BBC Hausa ta ruwaito. Har ila yau, Rahama ta shiga jerin mutanen da aka fi neman karin haske a kansu a shafin Google a shekarar 2020 a Najeriya, inda ta zo ta tara daga cikin mutane 10.
Bisa al’ada dama shafin Google kan fitar da kalmomi ko kuma sunayen da mutane suka fi lalubawa a shafin duk shekara a dukkanin kasashen duniya.
Bugu da kari kuma shafin kan yi wa sunayen rukuni ne, inda ake da rukunan mawaka da wakar kanta da wasanni da 'yan fim da fina-finan kansu da kuma tambayoyi. Ba abun mamaki bane don Rahama ta shhiga wannan jeri duba ga abun day a faru da ita a watan Nuwamba
na wannan shekara, inda aka samu cece-kuce tsakanin mutane a kanta bayan ta wallafa wasu hotuna dake nuna bayanta. Lamarin hotunan nata ya kara ta’azzara ne bayan an samu wani mutum da yayi kalaman da bai dace ba kan Annabi Muhammadu a wajen sharhi da ke karkashin hoton nata.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta shiga cikin jerin mutanen da suka fi tashe a intanet a 2020 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?