
Jama'a sun kauracewa zaben cike gibi a Legas da Plateau
Mutane sun kauracewa zaben cike gibin kujeran Sanatan Legas ta gabas da mazabar Kosofe a dukkan kananan hukumomi biyar dake karkashin mazabar. Akalla mutane 1,343,448 da suka yi rijista ake kyautata zaton zasu fito zabe a rumfuna 1,978 dake mazabar.
An bude rumfunan zaben misalin karfe 9 na safe amma mutane sun ki fitowa kada kuri'unsu, wakilin Daily Trust ya shaida. Yayinda ma'aikatan hukumar zabe ke zaune domin gudanar da abubuwa, mutane yan kalilan aka gani a rumfunan. Daily Trust ta kara da cewa misali a rumfar zabe ta 48 a gunduma ta shida, an bude rumfar zabe misalin karfe 9 amma mutane biyu kadai aka gani a wajen.
Plateau Hakazalika a jihar Plateau, mutane sun kauracewa zaben cike gibin Sanata Longjam da ya mutu. Daily Trust ta gano cewa a garin Yelwa, karamar hukumar Shendam, ma'aikatan INEC sun bude rumfunan zabe amma mutane sun ki fitowa yayinda wasu suka tafi harkokin gabansu. Misalin karfe 9 an safe, babu wanda aka gani yana niyyar kada kuri'a.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Jama'a sun kauracewa zaben cike gibi a Legas da Plateau "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?