
Ina mutanen suke ne? Ma'aikatan INEC na diban minshari saboda an kauracewa zabe
Mutane sun tafi harkokin gabansu duk da dokar hana sufurin motoci a wuraren da ake zabe - Wadanda ke zaune a gida kuwa sun yi amfani da hakan wajen hutawa da iyalansu
Mafi akasari sun ki fitowa zaben cike gurbin kujerun yan majalisu Ma'aikatan hukumar gudanar da zaben kasa, INEC, na diban minsharinsu ranar Asabar a Ikorodu yayinda mutane suka ki fitowa zaben maye cike gibin kujeran sanata mai wakiltar Legas ta gabas.
Yawancin matasan masu matsakaicin shekaru da suka yi zanga-zangan EndSARS sun ki fitowa kada kuri'unsu. Saboda haka, jami'an INEC suka dukufa suna baccinsu. Ina mutanen suke ne? Ma'aikatan INEC na diban minshari saboda an kauracewa zabe.
A bangare guda, mutane sun kauracewa zaben cike gibin kujeran Sanatan Legas ta gabas da mazabar Kosofe a dukkan kananan hukumomi biyar dake karkashin mazabar. Akalla mutane 1,343,448 da suka yi rijista ake kyautata zaton zasu fito zabe a rumfuna 1,978 dake mazabar.
An bude rumfunan zaben misalin karfe 9 na safe amma mutane sun ki fitowa kada kuri'unsu. Yayinda ma'aikatan hukumar zabe ke zaune domin gudanar da abubuwa, mutane yan kalilan aka gani a rumfunan.
Hakazalika a jihar Plateau, mutane sun kauracewa zaben cike gibin Sanata Longjam da ya mutu. Daily Trust ta gano cewa a garin Yelwa, karamar hukumar Shendam, ma'aikatan INEC sun bude rumfunan zabe amma mutane sun ki fitowa yayinda wasu suka tafi harkokin gabansu.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Ina mutanen suke ne? Ma'aikatan INEC na diban minshari saboda an kauracewa zabe "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?