
Hotunan ranar daurin auren jarumi Nuhu Abdullahi da zukekiyar amaryarsa
Jarumin masana'antar Kannywoood Nuhu Abdullahi, ya angwance da zukekiyar amaryarsa - Jarumin ya wallafa kyawawan hotunansa da sabuwar amaryarsa a shafinsa na Instagram
Ya kara da wallafa hotunan wurin daurin aure tare da abokai, 'yan uwa da abokan sana'arsa Fitaccen jarumin masana'antar fina-finan hausa, Nuhu Abdullahi, ya angwance da kyakyawar amaryarsa Siyama.
An daura auren kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a ranar Juma'a, 4 ga watan Disamban 2020. Kafin ranar aduarin auren, an fara ganin hotunan jarumin tare da kyakyawar amaryarsa na kafin aure suna yawo a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.
Jaruman masana'antar tare da masoyan jarumin sun dinga masa kyawawan addu'o'i tare da fatan alheri. A ranar Alhamis sai ga hotunan shagalin kamun auren da aka yi tare da kyakyawar amaryarsa.
Bayan daurin auren da aka yi a masallacin Juma'a na Alfurqan da ke Alu Avenue a GRA Nasarawa da ke jihar Kano, an ga hotunan jarumin da 'yan uwa tare da abokan arziki. Ya wallafa hotunan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Instagram inda aka ga jarumi Ibrahim Maishunku tare da Malam Aminu Saira a wurin daurin aure.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Hotunan ranar daurin auren jarumi Nuhu Abdullahi da zukekiyar amaryarsa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?