--
Hotunan baturen dan sanda a Najeriya sun haifar da cece-kuce

Hotunan baturen dan sanda a Najeriya sun haifar da cece-kuce


An hango wani bature farar fata cikin kayan ƴansanda bayan an watsa su a shafin sadarwar na Tuwita - Wani mai amfani da shafin Tuwita wato @AfamDeluxo shine ya watsa hotunan a shafinsa,sai dai ba kowa ne ya yarda cewa jami'in ƴansanda bane 


A ɗaya daga cikin hotunan da aka watsa,an ga mutumin yayi tsaiwa irinta jami'an ƴansanda Ganin wani bature farar fata ya jawo cece kuce a kafafen sadarwa na zamani bayan hotunansa cikin damara da kakin 'yan sandan Najeriya sun karaɗe yanar gizo. 


A ɗaya daga cikin hotunan, an hangi mutumin ya tsaya da wani jami'in ƴan sanda. Wasu masu amfani da shafin sadarwar Tuwita sun yarda cewa an ɗauki farar fatar aikin ɗan sanda, amma Legit.ng Hausa ba zasu iya tabbatar da sahihancin ko farar fatar jami'in ɗan sanda Najeriya ba ne. 


Mutane sun maida raddin hotunan tare da tofa albarkacin bakinsu a kan hotunan. Wasu kuma sun yarda farar fatar jami'in ƴan sanda ne, sai dai wasu basu gamsu ba. Wasu na ganin cewa, a nasu ra'ayin, ko kadan bai dace a dauki farar fata aikin dan sanda a Najeriya ba. 


A bangare guda kuma, wasu na ganin ba zai iya jure wahalar aiki da jama'ar Najeriya ba, musamman idan aka yi la'akari da kwatance da yadda aikin dan sanda ya ke da kima a turai da sauran kasashen da suka cigaba. 


Wani bangare na masu martani sun bayyana cewa akwai bakaken fata da ke aikin dan sanda a kasashen turai, a saboda haka mene ne abin mamaki idan farar fata ya zama dan sanda a Najeriya. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "Hotunan baturen dan sanda a Najeriya sun haifar da cece-kuce "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?