Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah
Wani direban mota ya basga wa jami'in LASTMA tabarya a kai a ranar Talata, 8 ga watan Disamba - Hakan ya faru saboda jami'in ya dakatar da direban a kan karya dokar tuki wuraren Jakande a Lekki
Tuni aka garzaya da direban ofishin 'yan sanda da ke Ilasan don daukar hukunci da bincike An kama wani direban mota, Fred Onwuche, saboda amfani da tabarya wurin ji wa wani jami'in LASTMA ciwo a Kosoko Rasak, wuraran Jakande a Lekki jihar Legas.
Al'amarin ya faru ne a ranar Talata, 8 ga watan Disamba kamar yadda wata takarda daga ofishin shugaban LASTMA, Olajide Oduyoye ta sanar. Ta tabbatar da yadda jami'in ya tsayar da direban saboda karya doka yayin tuki. Hakan ya fusata Onwenche, inda yayi gaggawar dakko tabarya ya buga wa kan jami'in LASTMA a kai, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
"An yi gaggawar tafiya da Rasaq asibiti don samun taimako na gaggawa sakamakon yadda jini yayi ta zuba saboda yankan. Sannan an tafi da Onwuche ofishin 'yan sanda da ke Ilasan don yanke masa hukunci da cigaba da bincike.
"Wajibi ne ya fuskanci fushin hukuma. Hukuma ba za ta saurara masa ba, don ya sanya abokai, 'yan uwa da iyalan Razak cikin takaici da bakin ciki," kamar yadda manajan yace. "Wannan ba shine karo na farko da ake kai wa jami'an LASTMA farmaki ba. Wasu daga cikinsu har kashesu suna kan aiki ake yi" cewar Oduoye.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Hotuna: Direba ya ragargaza kan jami'in LASTMA da tabarya, ya bar shi rai a hannun Allah"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?