Hattara: Hanyoyi 4 da za a iya 'sace' bayanan katin ATM ɗin ka
Tuesday, 29 December 2020
Comment
Yayin da yan Najeriya da dama ke ci gaba da fadawa hannun yan damfara, wasu masana harkar Intanet sunyi bayani kan yadda za a iya satar bayanan katin cirar kudi na ATM.
Sanin wadannan hanyoyin zai iya taimakawa al'umma su kiyayye kansu daga fadawa hannun bata gari masu satar bayannan mutane ko su yaudare su. Masanan sun bayyana haka a wata hirar da suka yi da jaridar The Nation.
A cewar jaridar, ma'aikatan banki sune da alhakin damfara ta hanyar katin ATM. Masanan sun bayyana hanyoyi daban daban da za a iya diban bayanan ATM din.
1. Za a iya saka wata na'ura a cikin ATM da zata iya daukar bayanan katin ya kuma tura musu daga baya ta yadda za su iya amfani da bayanan sirrin su cire kudi ko sayayya.
2. Mutane suna iya tsayawa a bayan mai amfani da ATM don ganin bayanai. Idan suka samu lamba katin da lambar sirri, za su iya amfani.
3. Mai amfani da PoS zai iya saka katin a cikin na'ura mai kama da injin PoS din amma kuma bayanan kati suke dauka.
4. Yayin siyayya ta yanar gizo wajen shigar da bayanan kati. Wasu lokutan, wasu mutanen na kirkirar shafin karya wajen domin mai siyayya ya shigar da bayansa na sirri da ke kati yayin da su kuma za su kwashe.
Kawai, zai nuna wa mutum "error" wato kuskure ba tare da sanin cewa an debi bayanai kuma za ayi amfani da su ba. Da suke karin bayani, masanan sun bayyana cewa yawancin damfarar ayyukan barayin yanar gizo ne amma zai matukar wahala kwarrarren masanin intanet ya dinga irin wannan ayyuka ta bayan fage.
Source: Legit
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Hattara: Hanyoyi 4 da za a iya 'sace' bayanan katin ATM ɗin ka"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?