Halima Abubakar: Likita yar arewa da ke neman miji a shafin soshiyal midiya
Wata likita yar Najeriya mai suna Dakta Halima Abubakar ta je shafin soshiyal midiya don neman mijin aure Matashiyar budurwar ta wallafa wani kyakkyawan hotonta a shafinta na Twitter sannan ta tambayi mabiyanta ko suna bukatar matar aure
Tuni bangaren sharhi na wallafar tata ya cika da martani daga mazan Najeriya wadanda suka nuna ra’ayi a kanta Wata likita daga yankin arewacin Najeriya ta je shafin soshiyal midiya don neman mijin aure, ta wallafa hotonta a shafinta na Twitter sannan ta tambayi mabiyanta ko suna bukatar matar aure.
Dr. Halima Abubakar tare da shafin Twitter @DrHalima_ ta sa mabiyanta tattaunawa kan kyakkyawan hotonta wanda ta wallafa tare da rubutu kamar haka: “Wa ke bukatar matar aure?”
Wani mai amfani da Twitter @AHMEDJEEKA ya rubuta: “Ina ganin ba daidai bane tallata kanki a idon duniya kina neman abokan rayuwa, haramun ne a Musulunce. Mutum irina ina bukatar matar aure amma da irin wannan tallar, ina tsoro.”
@makoloumar1 ya wallafa: “Shin za ki auri talaka mai kishin nema? + zan iya ciyar dake da baki kulawa sannan zan ba farin cikinki da kwanciyar hankalinki muhimmanci.” @HerbertTruth ya yi martani da: “Ina a hanyar zuwa gidan mahaifinki. Zan zo da magabata na yanzu haka. Babu lokaci.” Ga sauran sharhin da aka yi:
✋
— Delan_ (@dee_nuz) December 10, 2020
Who needs a wife? pic.twitter.com/8iewmwLNxN
— Dr. Halima Abubakar (@DrHalima_) December 10, 2020
I'm a Doctor that's full of love ❤ pic.twitter.com/PGVUTAj7YM
— Dr. Halima Abubakar (@DrHalima_) December 11, 2020
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Halima Abubakar: Likita yar arewa da ke neman miji a shafin soshiyal midiya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?