--
Hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Kano

Hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Kano


Har ila yau, ana asaran rayuka a titunan Najeriya sakamakon hadarin mota - Rashin kyawun hanya, karancin ma'aikata da kayan aiki babban tsaiko ne ga jami'an hukumar FRSC 


Direbobi na da nasu laifin na kure gudu a manyan hanyoyi Mummunan hadarin motan da ya faru a Kwanar Garko dake karamar hukumar Garko ta jihar Kano, ya yi sanadiyar halakar akalla mutane 11, Daily Trust ta ruwaito


Hadarin wanda ya faru daidai kauyen Dakare a hanyar Garko misalin karfe 10 na safiyar Alhamis tsakanin motoci biyu kirar Toyota Hiace da Volkswagen Sharon Mutane takwas sun mutu nan take yayinda wasu uku suka cika a asibiti bayan an kaisu jinya. 


An tattaro cewa yawancin matafiyan yan kasuwa ne da suke hanyar zuwa kasuwar Darki dake karamar hukumar Wudil. Tabbatar da labarin, kakakin hukumar kiyaye hanyoyi da hadura FRSC na jihar, Kabiru Daura, ya ce mutane 20 hadarin ya shafa kuma 6 na kwance yanzu a asibiti. 


A bangare guda, wani tsagin jam'iyyar APC a jihar Kano, a karkashin jagorancin Hussaini Isa Mairiga, ya sanar da sauke shugabannin tsagin jam'iyyar a karkashin jagorancin Abdullahi Abbas, kamar yadda Thecable ta rawaito. 


An sake zaben shugabannin tsagin jam'iyyar APC da ke karkashin jagorancin Abbas a shekarar 2018 saboda rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar a shekarar 2017. Tsagin da Abbas ya ke jagoranta shine mai daurin gindin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar ganduje. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?