Gwamnatin tarayya ta na amfani fasahar Isra'ila wajen leken asirin wayoyin 'yan Nigeria
Rahoton cibiyar Lab Citizen ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na kutse da leken asiri a wayoyin hannun jama'a - Lab Citizen, cibiyar kasar Canada, ta ce Nigeria da sauran wasu kasashen duniya sun sa yi manhajar leken asiri ta Circles
A cewar rahoton, Cirlcles reshe ne na kamfanin NSO, mai alaka da Isra'ila, da ke samar da manhajojin leken asiri da hukumomi ke amfani da su Wani rahoto da wata cibiyar binciken kutse da leken asiri da tabbatar da adalci a amfani da fasahar zamani ta wallafa ya nuna cewa hukumar leken asiri ta kasa ta na yi wa 'yan kasa leken asiri a wayoynsu na hannu.
Cibiyar mai suna 'Citizen Lab', da ke Toronto a kasar Canada, ta sanar da hakan ne cikin rahoton da ta fitar ranar Talata, kamar yadda Aminiya ta wallafa. Rahoton, wanda Citizens ta wallafa a shafinta, ya nuna cewa akalla hukumomi biyu ne, mallakar gwamnatin tarayya, ke amfani da fasahar leken asirin.
"Bincikenmu ya gano cewa akwai hukumomi biyu da ke amfani da manhajar ta kamfanin Circles mai alaka da kasar Isra'ila.
"Akwai wurare biyu da mu ka gano turakun manhajar a Najeriya, mun gano daya a wurin da muka taba gano manhajar Finfisher mai nasa da Circle a shekarar 2014. "Daya Kuma binciken adireshinta ya nuna tana sashen tattara bayanan sirri na hedikwatar rundunar tsaro (DIA) da ke unguwar Asokoro, Abuja.
Rahoton ya kara da cewa Najeriya na cikin kasashe 24 da suka sayi na'urori da manhajaojin leken asiri domin kutse cikin wayoyin hannu na 'yan adawa, ma su bore, 'yan jarida da ma tsageru. Manhajar Circle, wacce reshe ce ta kamfanin NSO, ta na bawa hukumomi damar yin kutse cikin wayoyin mutane tare da sarrafa wasu tsarin aiyukan wayar mutum kamar daukan hoto da sarrafa na'urar sauti.
Ya zuwa yanzu gwamnatin tarayya ba ta ce uffan akan rahoton Citizen Lab ba, wanda a cikinsa aka bayyana cewa 'yan gwagwarmaya na fuskantar barazana sakamakon leken asirinsu da hukuma ke yi mu su. A baya Legit.ng Hausa ta wallafa labarin cewa babban hafsan rundunar soji, Janar Tukur Buratai, ya gargadi manyan sojoji a kan juyin mulki.
Buratai ya ce dimokradiyya ta zo kenan, zama daram, a saboda haka lokacin katsalandan daga wurin sojoji ya wuce. Buratai ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin da ya ke gabatar da jawabi bayan ya kammala daura damarar kara girma ga sabbin manyan sojoji 39 da aka karawa girma zuwa mukamin manjo janar.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Gwamnatin tarayya ta na amfani fasahar Isra'ila wajen leken asirin wayoyin 'yan Nigeria"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?