
Gazawar shugaban kasa wurin bada tsaro abu ne da zai sa tsigesa, Osinbajo a 2015
Tuesday, 1 December 2020
Comment

Sakamakon kashe-kashen da 'yan Boko Haram suke yi a Najeriya, mutane sun yi wani waiwaye adon tafi - 'Yan Najeriya sun tunatar da mataimakin shugaban kasa, Osinbajo wata wallafa da yayi a Twitter a 2015 lokacin yana kamfen
A ranar 8 ga watan Fabrairun 2015 ne Osinbajo yace in dai Jonathan bai iya kare rayukan al'umma ba, ya cancanci a tsige shi Sakamakon kashe-kashen da 'yan Boko Haram suke tayi a Najeriya, 'yan Najeriya sun tunatar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a kan wata wallafarsa da yayi a 2015 a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.
Lokacin da Osinbajo yake kamfen a 2015, ya wallafa; "Idan shugaban kasa yace ba zai iya kulawa da rayuka da kuma dukiyoyin al'umma ba, tabbas laifi ne da yayi wanda ya cancanci a tsigeshi."
Ya yi wannan wallafar ne a ranar 8 ga watan Fabrairun 2015, wanda mutane suka yi ta tsokaci suna yabonsa. A ranar Asabar, mayakan Boko Haram sun kashe fiye da mutane 43 a wata gonar shinkafa da ke kusa da Maiduguri jihar Borno, Vanguard ta wallafa.
Kamar yadda AFP ta ruwaito, Boko Haram da ISWAP sun fara kai wa manoma, makiyaya da masunta hari, inda suke zarginsu da leken asiri da sanar da labaransu ga sojojin Najeriya, shiyasa sojojin suke kai musu farmaki.
A watan da ya gabata, AFP ta ruwaito yadda 'yan Boko Haram suka yi wa wasu manoma 22 yankan rago suna tsaka da noman rani a kusa da Maiduguri a hare-hare 2 daban-daban. Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammad, ya ce yanzu haka Najeriya tana hannun 'yan ta'adda suna yadda suka ga dama saboda an hana Najeriya makamai don yakar 'yan ta'adda.
SOURCE: LEGIT
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Gazawar shugaban kasa wurin bada tsaro abu ne da zai sa tsigesa, Osinbajo a 2015"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?