
Gagarumin rikici ya barke bayan 'yan daba sun fada kotu tare da fatattakar alkali da lauyoyi
An tsananta tsaro a harabar babbar kotun tarayya da ke Yenagoa saboda gudun 'yan ta'adda - A ranar Alhamis da ta gabata ne 'yan ta'adda dauke da makamai suka afka wa kotun, inda suka fatattaki lauyoyi
Sun yi kaca-kaca da duk wasu takardu da abubuwan amfanin kotun, sun kuma sace kudade da wayoyi An tsananta tsaro a harabar babbar kotun tarayya da ke Yenagoa, jihar Bayelsa a ranar Juma'a don gudun kutsawar 'yan ta'adda kamar yadda suka yi a ranar Alhamis da rana.
'Yan ta'addan da ke dauke da miyagun makamai, wadanda yawansu ya kai 20, inda suka fi karfin jami'an tsaro kuma suka kutsa cikin kotu mai daraja ta II, wacce take kula da tsayar da 'yan takarar jam'iyyar APC da na PDP a Bayelsa ta tsakiya.
Sun lalata duk wasu abubuwa masu muhimmanci na ofishin da ake ajiye kayan shari'ar da kuma kayan amfanin kotun, Vanguard ta wallafa. 'Yan ta'addan sun fatattaki lauyoyi da ma'aikatan kotun, sannan sun kwashe kudade, wayoyi da sauran abubuwa masu daraja.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Gagarumin rikici ya barke bayan 'yan daba sun fada kotu tare da fatattakar alkali da lauyoyi "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?