--
Fada a kan budurwa: An kashe mutum 1, jama'a masu yawa sun jigata

Fada a kan budurwa: An kashe mutum 1, jama'a masu yawa sun jigata


Rikici ya barke tsakanin wasu matasa biyu a garin Jalingo duk a kan budurwa - Daga bisani rikicin ya sauya salo inda ya koma na addini tsakanin kiristoci da musulmi 


gaggawar zuwan jami'an tsaro yankin yasa aka rasa rai daya kuma wasu suka jagata Wani mugun fada da aka yi a kan soyayyar budurwa ta sa an kashe mutum daya a Jalingo, babban birnin jihar Taraba. Gidan talabijin na Channels ya ruwaito yadda aka yi fadan a yankin gidan ruwa na Jalingo wanda ya janyo asarar kadarorin miliyoyin naira. 


An gano cewa fadan ya koma na addini saboda daya daga cikin samarin ya yi hayar 'yan daba domin tada hankula. Dayan saurayin kuwa ya kira abokansa ne domin su taimaka masa samun nasara. 


Amma kuma lamarin ya lafa bayan da jami'an tsaro suka isa yankin. Wani dan kasuwa wanda ya kware a aikin biredi mai suna Salihu Sale, ya ce "Lamarin ya fara a kwanaki hudu da suka gabata bayan karamin rikici ya barke. 


Ya zama gagarumin fada tsakanin matasan yankuna biyu a kan budurwa. "Daga baya ya koma rikicin tsakanin Kiristoci da Musulmi matasa. Sun dinga balle tagogi da kofofi amma kuma daga bisani jami'an tsaro sun isa inda suka shawo kan lamarin." 


Wani ganau ba jiyau ba mai suna Ezekiel Ali ya ce: "Duk da ni ba kwararre bane, daga abinda na gani shine, an harbi daya daga ciki kuma na ga ramukan harsashi a jikinsa." 


Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ahmed Azare, wanda ya ziyarci yankin ya kushe lamarin kuma ya ce mutum daya tak aka kashe. 


Azare ya bayyana cewa an kama wasu masu hannu a lamarin. Ya ce, "Daga rahotannin da jami'ai na suka samu, mutum daya tak ya mutu amma wasu masu tarin yawa sun samu raunuka kuma suna asibiti ana duba su." 


SOURCE: LEGIT

Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "Fada a kan budurwa: An kashe mutum 1, jama'a masu yawa sun jigata "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?