Duba Dalilin da ya sa kakakin majalisar dokokin jihar Kano yayi murabus
Daily Nigerian ta ruwaito cewa 35 cikin mambobin majalisar dokokin jihar Kano 40, sun rattafa hannu domin tsige Kakakin majalisa da shugaban masu rinjaye ranar Talata.
Duk da cewa Kakakin da shugaban masu rinjayen basu bayyana dalilin da ya suka yi murabis ba, an tattaro cewa sun yi murabus ne gudun kada a tsige su a zaman ranar Talata. Wani mamban majalisan ya bayyanawa Daily Nigerian cewa su biyun gwamnan kawai suke yiwa hidima ba mambobi ba.
"Mun yi fito an fito da su ne saboda sun yi kasa a gwiwa wajen jin dadinmu wajen gwamna. A watanni goma da suka gabata mambobi basu samu kudin mazabunsu ba, da kudadenmu da dama. Har alawus na ma'aikatan majalisa ba a biya ba na tsawon shekara daya, yace.
Kun ji cewa Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, AbdulAziz Gafasa, da wasu mutane biyu cikin shugabannin majalisan sun yi murabus daga kujerunsu.
Gafasa ya bayyana niyyarsa da magatakardan majalisan a wasikar da ya aike jiya, 14 ga Disamba, 2020. Wani sashen jawabin yace: "Ni, Rt. Hon. Abdulaziz Garba Gafasa na sanar da kai, mambonin majalisa da jama'a gaba daya cewa na yi murabus daga matsayina na kakakin majalisa daga ranan nan bisa wasu dalilai na kaina."
"A karshe, ina gidoya ga dukkan mambobin majalisan bisa goyon bayan da suka bani a lokacin da nayi matsayin Kakaki, kuma ina addu'a Allah Subhanahu wata’ala ya shiryar da sabbin shugabannin." Wadanda suka yi murabus tare da shi, a cewar majiya, sune shugaban masu rinjaye, Kabiru Dashi, da mataimakinsa, Tasiu Zabainawa.
Source: Legit.ng
0 Response to "Duba Dalilin da ya sa kakakin majalisar dokokin jihar Kano yayi murabus "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?