Duba cikin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan mai AC, wurin caji da bandaki kayatacce
Wednesday 23 December 2020
Comment
Wani kwastoma ya bayyana yadda jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya janyo cece-kuce da jinjina a kasar nan - Kamar yadda mutumin ya wallafa a shafinsa na Twitter, ana siyan tikitin 2,500 kuma ana samun matukar natsuwa
A yayin da jama'a da dama suke cewa tikitin ya yi tsada, wasu na ta jinjinawa wannan cigaban da zai maye gurbin tituna Yanayin tsarin sufurin Najeriya zai iya zama mai inganci a yadda aka fara kaddamar da jiragen kasa.
Jiragen kasa da za su dinga yawo daga Legas zuwa Ibadan a saukake ba tare da tunanin cunkoso ko lalatattun tituna ba abun dadi ne. A wata wallafa da wani ma'abocin Twitter mai suna @dmIdavies yayi a ranar Talata, 22 ga watan Disamba, ya bayyana yadda ya hau jirgin kasa da kuma yadda ya tarar da shi.
Kamar yadda ya wallafa tare da hotunan tikitinsa, daga tashar Yaba a Legas zuwa Moniya da ke Ibadan ana karbar N2,5000. Ya ce akwai tarin natsuwa a cikin jirgin kasan don har da AC wanda dole mutum ya ce a rage masa rabarsa akwai.
Akwai wuraren caji inda ko aiki ne mutum zai iya farawa kafin isa ofishinsa. Ya ce akwai abubuwa da yawa masu matukar inganci. Akwai inda jirgin ke tsayawa a Abeukuta a kan hanyarsa ta zuwa Ibadan, hakan yasa tafiyar take zama ta tsayin sa'o'i biyu da rabi.
It was clean, comfortable, and well air conditioned (maybe too well cause it was almost freezing at a point)
— Damz (@dmldavies) December 21, 2020
There were charging points and it left exactly when it was scheduled to.
Jirgin kasan yana aiki ne sau daya a kowacce rana, yana barin Ibadan zuwa Legas da karfe 8am ya isa da karfe 10:30am sannan ya koma Ibadan daga Legas da karfe 4pm zuwa 6:30pm. Domin samun tikitin, ana baukatar shaidar mutum amma a halin yanzu ba a yi ta yanar gizo.
Source: Legit
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Duba cikin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan mai AC, wurin caji da bandaki kayatacce"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?