--
Dokar majalisa: Shugaban kasa zai fuskanci barazanar tsigewa kan jinkiri wajen kafa majalisa

Dokar majalisa: Shugaban kasa zai fuskanci barazanar tsigewa kan jinkiri wajen kafa majalisa

Majalisar wakilai na neman gabatar da wani kudiri da zai tursasa zababben shugaban kasa ko gwamna bayyana yan majalisarsa cikin kwanaki 30 bayan karban mulki - Sabuwar dokar na kuma neman majalisa ta tsige duk shugaban kasa ko gwamnan da ya gaza aikata hakan ba tare da kwakwaran dalili ba 



Mista Kpam Sokpo ne ya gabatar da wannan batu a zauren majalisar a ranar Laraba Majalisar wakilai na neman sabon shugaban kasa ko gwamna ya kafa majalisarsa cikin kwanaki 30 bayan rantsar da shi ko ya fuskanci barazanar tsigewa daga majalisar dokokin tarayya ko na jiha, jaridar Punch ta ruwaito. 


Dokar mika mulki da hawa kujerar mulki, 2020, Mista Kpam Sokpo ne ya gabatar da ita inda a cikinta ne wannan bukata yake, ya kuma gabatar da shi a majalisa ne a ranar Laraba. Dokar ta kuma nemi a samar da kudade na musamman ga kwamitin mika mulki da kuma tursasa gwamnonin jiha sanar da yan majalisunsu a cikin wannan lokaci. 


Ya zo kamar haka: “Bisa ga sassa na 147 da 302 na kundin tsarin mulki, da zaran shugaban kasa ya kama aiki, zai nada ministoci cikin kwanaki 30 daga ranar da ya karbi rantsuwar kama aiki.


“Shugaban kasar zai kafa tare da nada dukkanin gwamnatocin hukumomi da masana’antun da suka isa ayi nade nade cikin watanni biyu daga ranar da ya karbi mulki. “A inda Shugaban kasar ya gaza ba dokokin hadin kai ba tare da kwakwaran dalili ba, toh za a kama shi da laifin saba ka’ida kamar yadda yake a karkashin sashi na 143(2) na kundin tsarin mulki.”


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Dokar majalisa: Shugaban kasa zai fuskanci barazanar tsigewa kan jinkiri wajen kafa majalisa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?