Diyar Sheikh Ibraheem Nyass Ta Rasu
Diyar shugaban darikar Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass, Sayyada Maryam Sheikh Inyass, ta rasu a kasar Senegal - Marigayiyar ta kasance mai hidima tare da sadaukar da rayuwarta wajen harkokin da suka shafi addinin Musulunci Sayyada Maryam Sheikh Ibrahim Inyass, diya wurin shugaban darikar Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Inyass, ta rasu a kasar Senegal
Kamar yadda Daily Trust ta tabbatar. Marigayiya Maryam ta kasance mai hidima tare da sadaukar da rayuwarta wajen harkokin da suka shafi addinin Musulunci, lamarin da ya sa ake mata lakabi da 'Hadimar Qur'ani'.
A nan gida Najeriya, annobar cutar korona ta zama sanadiyyar mutuwar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom a karkashin mulkin soja, Air Commodor Idongesit Nkanga, a ranar Alhamis, kamar yadda NewswireNGR ta rawaito.
NewswireNGR ta rawaito cewa gidan talabijin na Channels ya wallafa cewa tsohon gwamnan ya rasu yana da shekaru 68 a wani asibiti da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom. Ba'a bayyana sunan asibitin ba.
Marigayi Nkanga ya kasance gwamnan jihar Akwa Ibom daga watan Satumba na shekarar 1990 zuwa watan Janairu na shekarar 1992 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).
Kafin rasuwarsa, marigayi Nkanga ya na rike da shugabancin kungiyar kishin yankin kudu maso kudu, Neja-Delta (PANDEF).
Source: Legit
0 Response to "Diyar Sheikh Ibraheem Nyass Ta Rasu"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?