--
Dawowar korona: El-Rufa'i y umarci rukunin wasu ma'aikata su fara aiki daga gida daga Ranar Litinin

Dawowar korona: El-Rufa'i y umarci rukunin wasu ma'aikata su fara aiki daga gida daga Ranar Litinin

Gwamnatin jihar Kaduna ta kara dauki mataki na gaba bayan sanar da rufe makarantu da wuraren taron biki da gidajen rawa - A wani sako da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya fitar ya sanar da cewa ma'aikata kasa da mataki na 14 su cigaba da zama a gida 


Kaduna na daga cikin jihohin da ake ake samun hauhawar alkaluman masu kamuwa da korona a kowacce rana a 'yan kwanakin baya bayan nan A makon da ya gabata ne Legit.ng ta wallafa rahotanni a kan wasu jihohi da suka sanar da rufe makarantun firamare da sakandire saboda fargabar dawowar annobar cutar korona a karo na biyu. 



Gwamnatin jihar Kaduna ce ta fara fitar da sanarwar cewa ta rufe makarantu kafin daga bisani ta sanar da cewa ta bayar da umarni rufe wuraren taron bikin da gidajen rawar disko. 


A cewar El-Rufa'i, "bugu da kari a kan matakan da aka dauka a makon da ya gabata, gwamnatin jihar Kaduna (KDSG) ta umarci ma'aikata daga kasa da mataki na agidajensu daga ranar Litinin, 21 ga watan Disamba. 


"Gwamnatin jihar Kaduna ta na kira ga mazauna jihar akan su kula tare da kara da lura da biyayya ga dukkan matakan kare kai daga kamuwa da yada kwayar cutar korona, yin hakan alhakin kowa da kowa ne." 


A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umarnin rufe dukkan wasu wuraren taron biki, gidajen rawar disko, da cibiyoyin motsa jiki, a wani yunkuri na dakile yaduwar kwayar cutar korona a karo na biyu. 


Kazalika, gwamnatin ta takaita harkokin wuraren sayar da abinci; babu zama a ci, sai dai a kunshewa mutum abincinsa ya tafi da shi, kamar yadda Daily Trust ta rawaito. 


Bugu da kari, an umarci direbobi su rage yawan mutane da kaso 50 tare da tabbatar da cewa duk fasinjoji sun saka takunmi da kuma tabbatar da nesantar juna. 


Source: Legit 


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Dawowar korona: El-Rufa'i y umarci rukunin wasu ma'aikata su fara aiki daga gida daga Ranar Litinin "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?