--
Da kudin siyan iPhone 12 Pro Max, matashi ya bude gagarumin wurin siyar da tsire

Da kudin siyan iPhone 12 Pro Max, matashi ya bude gagarumin wurin siyar da tsire

Wani saurayi mai suna Asim Balarabe Yazid ya yi wata wallafa a kafar sada zumunta, dalilin haka mutane suka yi ta yaba masa - Asim ya ce ya fara sana'ar gasa nama a Kano, inda ya dauki masu taya shi aiki mutane 3 


Ya yi amfani da kudin da yakamata ya siya waya IPhone 12 Pro Max wurin fara sana'ar Wani saurayi mai suna Asim Balarabe Yazid ya baiwa matasa kwarin guiwa, inda yace maimakon mutum ya warware kudade masu yawa ya siya waya, gara yayi amfani da kudaden don ya fara sana'a dasu. 



A cewarsa, har daukar ma'aikata 3 yayi suna aiki a karkashinsa. Ya ce sana'arsa tana ta bunkasa, yanzu haka yana da kudaden da zaiyi amfani da su ya biya ma'aikatansa na watanni 3. Kuma yace yana adana ribar da yake samu maimakon kashewa gaba daya. 


'Yan Najeriya da dama sun yaba wa irin tunaninsa, inda suka ce ya yi kokari kwarai da yayi wannan tunanin. 


Wani Abba_GT cewa yayi, "Wannan alama ce ta wanda ya san naira ta lalace, kuma hakan ya faru ne sakamakon yadda muke amfani da kudadenmu ne, ba gwamnati kadai ba. "Idan da a kalla matasa 40% za su yi irin wannan tunanin na shi, da komai ya canja." 




 Da sauran mutane da suka yi ta yaba wa dabararsa da kuma yi masa fatan alheri. 


Source: Legit.ng 


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 08033293753


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Da kudin siyan iPhone 12 Pro Max, matashi ya bude gagarumin wurin siyar da tsire"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?