--
Da duminsa:Dr Isa Pantami ya yi umurnin dakatad da sayar da sabbin layukan waya

Da duminsa:Dr Isa Pantami ya yi umurnin dakatad da sayar da sabbin layukan waya


Hukumar sadarwan Najeriya, ta umurci dukkan kamfanonin sadarwa su dakatad da rijistan sabbin layukan waya a fadin tarayya. NCC ta bayyana hakan ne a jawabin da diraktan yada labaranta, Dr. Ikechukwu Adinde, ya saki ranar Laraba. 


Jawabin yace hukumar ta bada umurnin haka ne bisa ga manufar gwamnatin tarayya na duba rumbun wadanda sukayi rijista da kuma tabbatar da cewa kamfanonin na bin ka'idoji da sharruda. Ta ce ya zama wajibi a dakatad da layukan wayan da ba'ayi rijista ba wajen ayyukan banza. 


A cewar jawabin: "Bisa ga manufar gwamnatin tarayya na cigaba da samun nasara wajen rijistan layukan waya, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, ya umurci hukumar ta kaddamar da binciken rumbun rijista." 


"Manufar wannan bincike shine tabbatar da cewa an bin ka'idoji da sharrudan da aka gindayawa kamfanonin sadarwa." "Wannan umurni na da muhimmanci saboda yawaitan layukan waya da ba'ayi rijista ba kuma ake amfani da su wajen ayyukan laifi."


"Saboda haka, ana umurtan kamfanonin sadarwa su dakatad da sayar da sabbin layuka da rijista har sai an kammala bincike." "Za'a kwace lasisin duk kamfanin sadarwan da bai bi wannan umurni ba." 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Da duminsa:Dr Isa Pantami ya yi umurnin dakatad da sayar da sabbin layukan waya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?