Da duminsa: Pantami ya bada umurnin rufe layukan marasa lambar katin zama dan kasa
Daga cikin matakan kawo karshen tabarbarewan tsaro a Najeriya, ma'aikatar sadarwa ta yanke shawaran duba layukan waya
Ana bukatan kowa yayi katin zama dan kasa kuma ya hada da layin wayansa Gwamnatin tarayya ta bada umurni ga dukkan kamfanonin sadarwa su rufe layin wayan duka wanda bai hada layinsa da lambar katin zama dan kasa nan da ranar 30 ga Disamba, 2020.
Wannan umurni ya biyo bayan ganawar gaggawan masu ruwa da tsaki a sashen sadarwa da Minista, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami ya shirya ranar Litinin, 14 ga Disamba, 2020.
Bayan ganawar, an yi ittifakin cewa fari daga ranar Alhamis, 16 ga Disamba, 2020, dukkan kamfanonin sadarwa su bukaci mutane su hada layukan wayansu da lambar katin zama dan kasa.
The Nigerian Communications Commission (NCC) has given telecommunications operators (MTN, Glo, Airtel, 9Mobile and others) in the country two weeks to block all SIM cards that are not registered with the National Identity Numbers (NIN), the Commission has said in a statement.
— Bashir Ahmad (@BashirAhmaad) December 15, 2020
Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis tace an rage kudin 'Data' da kashi 50% bisa umurnin da aka baiwa hukumar sadarwan Najeriya NCC. Saboda haka, kudin 'Data' na 1GB ya sauko daga N1000 zuwa N487 daga yanzu ( tun watan Nuwamba), The Nation ta ruwaito.
'Data' kudi ne da mutum ke saya a domin amfani da samun shiga yanar gizo. Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami, wanda ya sanar da hakan ya ce, an yi hakan ne bisa umurnin da aka baiwa hukumar NCC na tabbatar da cewa an rage kudin 'data' a fadin tarayya.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Da duminsa: Pantami ya bada umurnin rufe layukan marasa lambar katin zama dan kasa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?