--
Da duminsa: Manyan hafsoshin soji 18 sun harbu da cutar korona

Da duminsa: Manyan hafsoshin soji 18 sun harbu da cutar korona

An gwada manyan hafsoshin sojin Najeriya, inda aka gano suna dauke da cutar COVID-19 


An gano hakan ne bayan sun koma daga wani taron sojoji na shekarar 2020 da aka yi Abuja 


Tuni NCDC ta umarci sauran sojojin da suka je taron, da iyalansu a kan su killace kansu na mako daya An gwada a kalla manyan hafsoshin sojin Najeriya masu mukamin janar guda 18 kuma aka gano suna dauke da cutar COVID-19, Channels TV ta wallafa. 



Ana zargin jami'an sojin sun yi cudanya da marigayi Manjo Janar Olu Irefin, wanda ya mutu sakamakon cutar COVID-19 makon da ya gabata. 


Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, wadanda aka gano suna dauke da cutar sun je taro shugabannin soji na shekarar 2020 da aka yi a wata cibiya a Abuja. 


Baya ga nan, an samu labarin yadda marigayi janar Irefin ya kaiwa abokan aikinsa ziyara kafin su je taron. 


A don haka, NCDC ta umarci sauran sojojin da suka halarci taron da kuma iyalansu da su kebe kawunansu na mako guda. 


Gidan talabijin din Channels sun bayyana yadda aka tabbatar an fesa magungunan da za su kashe kwayoyin cutar a dakin taron a kwanakin karshen mako. 


Dama janar Irefin ya fara ciwo ne a makon da ya gabata a wani taron sojoji da suka yi, wanda daga nan aka kai shi asibiti. Daga baya aka gano yana dauke da cutar COVID-19, ana cikin kulawa da lafiyarsa ya mutu. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Da duminsa: Manyan hafsoshin soji 18 sun harbu da cutar korona "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?