
Da duminsa: Gwamna ya dakatar da COS dinsa a kan yi wa fasto ruwan kudi a ofishinsa
Gwamnan jihar Abia, Dr Okezie Ikpeazu ya dakatar da shugaban ma'aikatansa - Hakan ya biyo bayan ganinsa a wani bidiyo yana lika wa wani fasto kudi, yana kwasar rawa
Bayyanar bidiyon ya janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya dakatar da shugaban ma'aikatansa,
Anthony Agbazuere. Bayan bayyanar bidiyon Agbazuere yana watsa wa Odumeje, 'Indaboski', kudi ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta, The Cable ta ruwaito.
A bidiyon an ga Agbazuere yana manna wa Chukwuemeka Ohanaemere wanda aka fi sani da Odumeje, wannan sanannen faston na Onitsha, yana kwasar rawa.
Duk da dai ba a san lokacin da aka dauki bidiyon ba, amma ko da gani Agbazuere yana kujerarsa. Jama'a sun dinga caccakrsu inda suka kalla hakan a matsayin almubazzaranci.
A wata takarda ta ranar Lahadi, Chris Ezem, sakataren gwamnan, inda aka tabbatar da dakatar da CoS take-yanke. Kamar yadda takardar tazo:
"Gwamnan jihar Abia, Dr Okezie Ikpeazu, ya umarci dakatar da shugaban ma'aikatan gwamnan daga ofishinsa, Dr ACB Agbazuere."
SOURCE: LEGIT
0 Response to " Da duminsa: Gwamna ya dakatar da COS dinsa a kan yi wa fasto ruwan kudi a ofishinsa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?