--
Da duminsa: An dawo da zanga zangar #EndSARS a garin Osogbo Na Jihar Osun

Da duminsa: An dawo da zanga zangar #EndSARS a garin Osogbo Na Jihar Osun


Matasa sun fara gudanar da sabuwar zanga zangar EndSARS a garin Osogbo, jihar Osun - Sun gudanar da gangamin ne a yau Litinin, 7 ga watan Oktoba inda suka yi tattaki har zuwa majalisar dokokin jihar 


Masu zanga zangar da ke kira ga shugabanci nagari da wasu bukatun sun nemi zantawa da shugabannin majalisar Wasu matasa karkashin inuwar gangamin #EndSARS, a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, sun gudanar da zanga zangar a Osogbo, babbar birnin jihar Osun. 


Sun yi gangamin ta cikin unguwannin Osogbo zuwa majalisar dokokin jihar Osun, inda suka bukaci tattaunawa da shugabannin majalisar, jaridar Punch ta ruwaito. 


Zanga zangar wanda Emmanuel Adebisi ya jagoranta na kira ga shugabanci nagari da sauran abubuwa. A wani labarin, mun ji cewa biyo bayan tsoro da ake yi na barkewar sabuwar zanga-zangar EndSARS, an tura jami’an yan sanda da na sojoji zuwa mashigin harabar Lekki Toll Gate. 


Masu ababen hawa da masu tafiya a kafa sun sanar da manema labarai cewa an zuba jami’an tsaro a wajen a safiyar ranar Litinin, 7 ga watan Disamba. 


Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya ki amsa kiran wayar da aka yi masa a safiyar yau Litinin. 


A wani lamarin kuma, wamnan jihar Legas, Babajide Sanwoolu, a ranar Alhamis ya bada milyan goma ga kowanne cikin matan jami'an yan sanda shida da aka kashe yayin zanga--zangan EndSARS. Gwamnan ya yi hakan ne domin cika alkawarin da yayi lokacin ganawarsa da yan sandan jihar. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Da duminsa: An dawo da zanga zangar #EndSARS a garin Osogbo Na Jihar Osun"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?