
Budurwar da ke samun kudin da bai ka N50,000 ba tana tamfatsa katon gida, ta janyo cece-kuce
Thursday, 3 December 2020
Comment

Wata budurwa ta wallafa hotunan katafaren gidan da ta gina da albashinta wanda yake kasa da N50,000 duk wata
Samke_nkwanyan ta wallafa hotunan a shafinta na Twitter, tana mai alfahari da ginin gidan da tayi da kanta
A cewarta, ta gina katafaren gidan da albashinta na watannni 4 duk da N49,948.22 ne albashinta Idan mutum yayi aiki tukuru, yana matukar alfahari wurin nuna wa duniya don a yi masa sam barka.
Wata Samke_nkwanyan ta bayyana hoton wani katafaren gida da ta dage ta gina.
A cewarta, sai da tayi watanni 4 tana aiki tukuru tukunna ta samu nasarar karasa ginin gidanta. Da albashinta R2,000 wanda yayi daidai da N49,948.22.
A cewarta, dama ta tara R10,000 daidai da N250,000 a asusunta. Sannan ta amshi bashin R5,000 wato N124,975, wanda ta gama biya a watan Augusta. Duk da tarin da tayi, ta zage wurin yin aiki tukuru.
Samke_nkwanyan ta ce ta bukaci taimakon 'yan uwa da abokan arziki amma suka ki taimaka mata. Wata Layne_JazzeySA ta rubuta: "Gaskiya gidan yayi kyau, gaskiya kin yi kokari.
Idan har da wannan albashin naki, kina iya gina gida, idan Ubangiji ya ciyar da ke gaba za ki iya yin manyan abubuwa. Cikin watanni 4, gaskiya kin yi kokari sosai."
tNaxe23 ya ce: "Ko karami ne ko babba, gidanki ne, kuma sunan ki zai amsa. Ki share duk wani wanda zai soke ki." Haka dai mutane suka yi ta tsokaci iri-iri na yabo da gwarzontakar budurwar.
Well i had 10k savings initially then i took a 5k loan which i paid back in monthly from August till December but the material wasn’t enough so i asked from friends and family they helped out 😍😊
— ❤🇿🇦Mazikode Samke🌼🌱 (@Samke_nkwanyan) December 1, 2020
SOURCE: LEGIT
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Budurwar da ke samun kudin da bai ka N50,000 ba tana tamfatsa katon gida, ta janyo cece-kuce"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?