--
Budurwa ta fusata bayan saurayinta da ya ci cacar N20m ya bata N20,000

Budurwa ta fusata bayan saurayinta da ya ci cacar N20m ya bata N20,000

Wata budurwa 'yar Najeriya ta wallafa irin takaicin da saurayinta ya sanya mata a zuciya - Ta ce ya sami N20,000,000 ta hanyar caca, amma ya rasa kudin da zai bata sai N20,000 



Budurwar ta ce a zaton ta zai warware a kalla N1,000,000 a cikin kudin ya bata Idan mutane 2 suna soyayya, batun kudi yana zama babbar matsala musamman idan daya daga cikin masoyan yana sanya mako a harkar. 


Wata budurwa mai suna Reddishwine3, ta wallafa irin takaicin da saurayinta ya sanya mata a zuciya a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter. 



A cewarta, saurayinta ya samu zunzurutun kudade har N20,000,000, a harkar caca. Maimakon ya cire a kalla N1,000,000 a cikin kudin ya bata, sai ya dauki N20,000 ya bata. 






Wannan abu da saurayin yayi ya fusata budurwar kwarai. Mutane da dama sun yi ta cece-kuce a karkashin wallafar, inda wata Lola Okunrin tace, "Kila saurayin bai damu da budurwar bane, har da ya kasa cire fiye da N20,000 a cikin kudin ya bata."


Wata Mimi, cewa tayi, "Gaskiya da saurayina ne da fiye da rabin kudin zai bani." Amma ta shawarci budurwar a kan tayi hakuri tun da ma ta samu ya bata wani abu cikin kudin. Ta ce wasu samarin ba za su baka ko sisi ba. Ta kwantar da hankali har itama ta samu nata N20,000,000 din.


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services ๐ŸŒ

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Budurwa ta fusata bayan saurayinta da ya ci cacar N20m ya bata N20,000 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?