
Bayan soyewa na shekaru 8 babu niyyar aure, budurwa ta maka saurayi a kotu
Wata mata ta maka saurayinta a kotu saboda ya ki mayar da hankali ya aureta duk da shekarunsu 8 a tare - A cewarta har haifa masa da daya tayi, amma har yanzu shiru ya bayar da sadakinta amma ya ki aurenta
Saurayin ya kare kansa, inda yace ba shi da isasshen kudin aurenta, sannan ba ta bashi cikakkiyar kulawa Wata mata ta maka saurayinta a kotu sakamakon bata mata lokaci duk da shekarunsu 8 tare amma ya gaza aurenta.
Ngoma ta sanar da wata kotu a Zambia cewa ta gaji da jiran Herbert Salaliki mai shekaru 28, wanda yayi mata alkawarin aure. A cewar Mwebantu, har yanzu Ngoma tana zaune da iyayenta duk da ta haifa wa Herbert da guda daya, shi kuma yana zaman kansa. Kamar yadda aka samu rahotonni, saurayin ya biya sadakin budurwar amma har yanzu bai aureta ba.
Ngoma ta bayyana cewa ta gaji da jiransa, shiyasa ta maka shi a kotu sakamakon yi mata wasa da rayuwarta. A cewarta: "Har yanzu ya ki mayar da hankali, shiyasa ta kawo kararsa a kotu saboda ya kamata a ce ta san inda ta dosa da rayuwarta."
Ngoma ta ce tana zarginsa da ha'intarta, bayan ta gano yana tura wa wata budurwa sako tana ganin wani abu yana faruwa tsakaninsu. Herbert ya kare kansa, inda yace bashi da isassun kudaden da zai iya aurenta, sannan ya ce Ngoma bata bashi cikakkiyar kulawa. Alkalin ya shawarcesu da suyi kokarin sasanta junansu, saboda har yanzu babu wata shaida ta aurensu.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Bayan soyewa na shekaru 8 babu niyyar aure, budurwa ta maka saurayi a kotu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?