--
Bayan neman yafiyar gwamnatin Ganduje: Kotu ta sallami shari’ar Naziru sarkin waka

Bayan neman yafiyar gwamnatin Ganduje: Kotu ta sallami shari’ar Naziru sarkin waka

 Kotu ta sallami shari'ar da take yi tsakanin Naziru M. Ahmad da gwamnatin jihar Kano - Wannan ci gaban na zuwa ne bayan sarkin wakar ya nemi yafiyar gwamnatin Abdullahi Ganduje 


An dai tuhumi shahararren mawakin ne da sakin wata waka tun ba a kai ga tantance ta ba Wata kotun majistare da ke zama a jihar Kano ta sallami shari’ar shahararren mawakin nan na masana’atar Kannywood, Naziru M. Ahmed.


 Hakan ya biyo bayan neman yafiyar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na jihar da mawakin yayi, sashin Hausa na BBC ta ruwaito. 


Kotun wacce mai shari’a Aminu Gabari ke shugabanta, ta rufe shari’ar sarkin wakar kan laifin fitar da wata waka ba tare da hukumar tace fina-finai ta Kano ta tantance ta ba. 


Hakan ne ya sa a watan Satumban 2019 aka kama Naziru Sarkin Waka amma daga bisani kotun ta sake shi bayan ya cika ka’idojin belin da kotun ta shimfida masa. Sai dai a farkon watan Nuwamba, kotun ta soke belin da aka bai Naziru inda ta shimfida masa wasu sababbin ka’idojin belin. 


Daga nan ne ta aike da shi gidan yari saboda rashin cika sharudan a kan lokaci, duk da cewa an gindaya masa su ne a kurarren lokaci, kamar yadda ya fadi. A zaman kotun na ranar Talata, lauyan gwamnatin Kano, Barista Wada Ahmad Wada ya gabatar da wata takardar bayar da hakuri ga gwamnatin jihar wadda ya ce daga hannun Naziru ta fito. 


A cikin takardar, wadda Sarkin Waka ya rubuta ta zuwa ga Kwamishinan labarai na jihar, ya ce "Ni Naziru M. Ahmed ina bayar da hakuri matuka bisa zargin da aka yi mini kuma ina dansanin abin da hakan ya haifar." 


Mawakin ya kara da cewa ya bayar da hakurin ne bayan masu ruwa da tsaki sun tsoma baki a cikin lamarin. Lauyan Naziru, Barista Sadik Sabo Kurawa, ya ce sun cimma wannan matsaya ce sakamakon fahimtar junan da aka samu daga bangarorin biyu. 


"Abin da ya faru a yau shi ne da ma an samu daidaituwa tsakanin bangaren gwamnati da na wanda ake kara, shi ya sa suka zo yau suka kawo karshen tuhume-tuhumen da ake yi masa suka wanke shi daga ciki," in ji shi. 


Daga nan ne Mai Shari'a Aminu Gabari ya sallami Naziru M. Ahmed sannan aka rufe shari'ar baki baya. A wani labarin, Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Rahama Sadau, ta yi martani a kan batutuwan da suka addabi kasar a yanzu. 


Jarumar ta bayyana cewa wannan ta zo da abubuwa da dama na kalubale wanda suka hada da Korona da matsalar tattalin arziki da kuma matsalar tsaro. Rahama ta kuma yi Allah-wadai da abinda ya faru a yankin arewacin kasar inda tayi kira ga mahukunta a kan su yi wani abu a kai cikin gaggawa. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "Bayan neman yafiyar gwamnatin Ganduje: Kotu ta sallami shari’ar Naziru sarkin waka"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?