--
Bayan kama ni da kwarto, mijina yana ta gwangwaje ni da kyautuka, Matar aure

Bayan kama ni da kwarto, mijina yana ta gwangwaje ni da kyautuka, Matar aure


Mijina ya fara yi min kyautuka na musamman bayan ya kama ni dare-dare a gado da kwarto, cewar wata mata aure - Har alkawarin tafiya da ita kasar ketare yayi don su sha shagalin kirsimeti tare, bayan ya umarci kwartonta da ya tafi



Yanzu haka ta shiga zullumin kada bayan sun tafi ya dauki wani mummunan mataki a kanta, shine take neman shawara Wani mutum dan South Africa ya kwantar da hankalinsa bayan ya kama matarsa da kwarto a gadonsu na sunnah, ya kuma zage wurin bata kyaututtuka na ban mamaki. 


Matar ta wallafa a kafar sada zumunta tana bukatar jama'a su bata shawara a kan rudanin da ta shiga, jaridar The Nation ta wallafa. .



Ta ce mijinta ya kama ta dare-dare a kan gado tare da kwarto suna lalata, maimakon yayi mata kaca-kaca, sai ya fara yi mata salo iri-iri na soyayya, kuma ya umarci kwartonta ya sanya sutturarsa ya wuce abinsa. 



A cewarta, ta yi zaton mijinta zai dauki tsauraran matakai a kanta, amma sai ya nuna mata cewa ba komai bane, hasali ma, ya koma bata kyautuka na musamman. 


A cewar matar, mijinta ya tsiri yi mata kyautuka iri-iri tun bayan ya kama ta da kwarton, sai dai hakan ya saka ta a zullumi. 


Ta bayyana yadda ta shiga tsananin tashin hankali bayan mijinta ya fara shirye-shiryen tafiya tare da ita kasashen ketare kafin lokacin bikin kirsimeti, sai dai, cike take da tsoro don kada ya dauki mummunan mataki a kanta idan sun tafi.  


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "Bayan kama ni da kwarto, mijina yana ta gwangwaje ni da kyautuka, Matar aure "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?